Kabiru Nakwango
Kabiru Nakwango ya kasance jarumi ne acikin dattawan masana antar fim ta Hausa wato kanniwud, Yana taka rawa a matsayin malami masanin alqur,Ani. kabiru yayi fina finai da dama a kanniwud, ya Dade Yana fim tsohon jarumi ne[1][2]
Takaitaccen Tarihin sa
[gyara sashe | gyara masomin][3][4]An haifi kabiru a ranar 2 ga watan fabrairu shekarar 1962, a Karamar hukumar dala jihar Kano a korafin kan giwa, daga shekarar 1967 zuwa 1971 yayi karatun islama bangaren addini musulunci, daga Nan ya shiga makarantar koyan larabci ta sakandari a shekarar 1972 zuwa shekarar 1975, mahaifin sa Alhaji Abubakar iyu (danbaba) da mahaifiyarshi hajiya fadinatu Nakwango, daga baya kuma ya sake koma was firamare school ta dama a shekarar 1975 zuwa shekarar 1980, a shekarar 1980 zuwa shekarar 1985 ne ya shiga makarantar (government commercial secondary school airport road) anan yayi karatun sakandiri, daga Nan ya fara koyar wa a matsayin malamin islamiyya a dala, ya Kuma Kara koyarwa a madarasatul _kirr,atu qur,an yake koyarwa kyauta fisabilillah daga shekarar 1985 zuwa shekarar 2000, suka dauke shi a matsayin malami, a shekarar 2001 zuwa shekarar 2004, ya shiga kwalejin Kano(FCE KANO) anan ya Sami kwalin NCE,[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-22. Retrieved 2023-07-22.
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/media-60044317
- ↑ http://hausafilms.tv/actor/kabiru_nakwango
- ↑ https://m.imdb.com/name/nm3955647/bio/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-22. Retrieved 2023-07-22.