Jump to content

Kacici-kacici

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
kacici-kacici
game genre (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na puzzle (en) Fassara da word game (en) Fassara
Bangare na small genre of folklore (en) Fassara
Has characteristic (en) Fassara oral tradition (en) Fassara

Kacici-kacici tsarin wasa ne domin wasa kwakwalwa da kuma samun raha a kasar Hausa, sunayi ne domin ilimantarwa ko fadakarwa, kacici-kacici yana zuwa ne ta sigar zance a dunmule, amma wacce take kunshe da amsa, kuma ana bukatan masu sauraro da su bada amsa akan maganar.[1]

Kacici-kcici yana da alaqa da wasa kwakwalwa, amman galibi suna da bambamci, wasa kwakwalwa ana yinshi ta sigar tambaya ko magana a zube,wanda shima kacici-kacici haka yake,sai dai kawai kacici-kacici ana cewa “Kacici-Kacici” idan za ayi,shi kuma wasa kwakwalwa farawa kawai akeyi. Sannan ana cewa “kulin kulifita” wanda wannan magana ce wacce bata da ma’anata sigar furuci, amman tana da amsa domin hausawa na cewa “Gauta”.[2][1] “Gauta”  alama ne dake nuna cewa zaka kasance cikin wasa.[2].

I.Y yahaya (1988b) ya kawo su dayawa a cikin littafin shi,[3][4]

s/n Kacici Kacici Amsa
1 Shanuna dubu madaurinsu daya.   Amsa: Tsintsiya
2 Baba na daka gemu na waje. Amsa: Hayaki
3 Rigata daya aljihunta dari.   Amsa: Gidan Tururuwa
4 Tsumagiyar kan hanya Fyadi yaro fyadi babba.         Amas: Yunwa
5 Riga fari wando fari Amsa: Balbela [5]
6 sauti, lafazi wajen yin wasan, misali: ƙurƙucif – ƙucif: Amsa:Kwanciyar kare[6]

Tana daga ciki hikimar tatsuniya, waƙa, kacici-kacici, fadakarwa, ilimantarwa da kuma nishadantarwa, amman galibin zancen a zukatan hausa alama ce na cewa wannan  cikakken bahaushe ne, kanacewar akwai makwaftan hausawa dake yaran hausa a cikin su. Yanayin iya furta kalmomin da sanin zantukan karin magana, kacici-kacici da hikayu, alama ne na kasancewar mutum bahaushe ne, kuma iya furucin suna kiranshi da “Gagara Gwari” Ga daya daga cikin wasu furruci wadanda ake tankwara harshe, kuma cikakken Mallam bahaushe ne kadai yake iya yin furucin.( “Da kwado da kato suka tafi koto. Kato yai koto, kato ne zai kwace ma kwado koto, ko kuwa kwado ne zai kwace ma kato koto?”[6]

  • Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. ISBN 978-1-4744-6829-9. OCLC 648578425.
  1. 1.0 1.1 Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute.p,81
  2. 2.0 2.1 kraff 1976b.
  3. Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute.p.5
  4. Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute.p,8
  5. I.Y yahaya (1988b),(p251)
  6. 6.0 6.1 Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute.p,82