Kamogelo Mampe
Appearance
Kamogelo Mampe (an haifeta 7 Disamba, shekarar alif 1985), ƴar kasuwa ce ta Afirka ta Kudu, kuma ƴar wasan kwaikwayo, mai gabatar shiri, MC sannan kuma kuma mai ɗora murya.[1] An fi saninta da rawar da ta taka a cikin jerin shirin talabijin Muvhango.[2]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Mampe a ranar 7 ga Disamba 1985 a Free State, Afirka ta Kudu. Ta sami horo a matsayin ƴar wasan kwaikwayo daga Performing Arts of the Free State (PACOFS) kuma daga baya ta kammala karatun digiri a fannin ilimin halayyar ɗan Adam.[3]
A shekarar 2007, ta yi ɗan gajeren dangantaka da mawakin Hip-hop Bongani Fassie, wanda ɗan marigayi Afro-pop diva Brenda Fassie ne.
Fina-finai
[gyara sashe | gyara masomin]Year | Film | Role | Genre | Ref. |
---|---|---|---|---|
2004 | Muvhango | Palesa | TV series | |
2006 | Heartlines: The Bet | Jacqui | TV series | |
2010 | Intersexions | Palesa | TV series | |
2013 | Isibaya | Nurse Ditsele | TV series |
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "GOING, GOING, GONE". Retrieved 2021-11-28 – via PressReader.
- ↑ "Muvhango Actress Calls It Quits: TVSA". www.tvsa.co.za. Retrieved 2021-11-28.
- ↑ "Kamogelo Mampe: TVSA". www.tvsa.co.za. Retrieved 2021-11-28.