Karancin Ruwa A Duniya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
saharab Algerian babu ruwa acikinta, koma dama yawance sahara ba a samu ruwa

Karancin Ruwa A Duniya Lokacin da rijiya ta karfe ne, muke sanin darajar ruwa,” kamar yadda Benjamin Franklin, kaya daga cikin iyayen kasar Amurka, fiye da karni biyu da suka wuce, ya lura, tun kafin wani ya yi tunanin bukatar tanadin wani tsarin ajiyar ruwa, ko ruwa mai tsabta na iya karanci, a fadin wannan duniyar. A yau, a karo na farko, a tarihin bil-adama, “rijiyar duniya” ta fara kafewa kuma duk za mu san zafin abinda zai faru, lokacin da al’umma suka fara rasa babban abinda ya fi komai amfani, a rayuwa. Kamar yadda danyen mai ya sake wa duniya fasali, da kuma tarihi, a karni na 20, haka rikicin rashin ruwa mai tsabta zai fara sake fasalin siyasar muhalli, da tattalin arziki da kuma makomar duk wata wayewar bil-adama, a ƙarni na 21. Bugu da kari, domin shi ruwan, ba kamar danyen mai ba, ba za a iya sake maido shi ba: Ba za mu iya shan danyen mai ba, ko mu shuka shi, kamar abinci.

Abinda ke faruwa, musamman, shi ne, duk da mugun matsin da ba za mu iya cimma biyan bukata ba, game da wannan yanayin, na wannan zamanin wanda ya rubanya yin amfani da ruwa, bisa ga irin yadda yawan jama’a ke hauhawa muna karancin duk wani yunkuri na dorewar tanadin isasshen abinci, da makamashi, da masana’antu, da muke bukata, kazalika da yawan ruwan da jama’a miliyan dubu shida da miliyan 900, ko kasa da haka, don yin amfani da shi a gidaje, bayan a halin yanzu, ana da bukatar shayar da mutane miliyan dubu tarra, nan da zuwa shekarar 2050. Rikice-rikice, na ta kara abkuwa, bisa ga gagarumin rashi da kuma barnar da muke yi, ta ruwa, a kusan ko’ina. Irin yadda karancin ruwan ke faruwa da bil-adama, a halin yanzu, da kuma wata kalubalen, mai harshen damo  a dayan bangaren da kuma na siyasa, a dayan gefe. A sakamakon rashin daidaituwar yadda ake rarraba ruwan mai tsabta, a duniya, da kuma irin yadda yawan jama’a ke kara matsa lamba, da kuma irin yadda ake samun akasin fadada al’amurran jama’a, a fadin duniya, dangane da “masu” ruwan da “marasa shi”  a duniya, da kuma sauran kasashe, har ma a tsakanin kungiyoyi, da sassa, da ma jinsin harkokin tattalin arzikin da suka da]e, suna gasar samun daidaita albarkatun ruwa.

Ruwa da Hauhawar Wayewar Kai[gyara sashe | gyara masomin]

Harkar kula da albarkatun ruwa, ta kasance kan gaba, wajen harkokin mulki, da wadata, da kuma nasarorin bil-adama. A cikin shekarun karnin da suka wuce, al’umma sun yi fafitikar siyasa, da soja, da kuma tattalin arziki, da ma fasaha, domin mamaye albarkatun ruwan duniya. mun yi hakurin kakkafa garuruwa, a zagayenmu, da kuma safarar kayayyaki, domin cin gajiyar duk wani makamashi, ta fannoni da dama, da kuma yin amfani da gagarumar fa’idar aikin noma, da masana’antu, da kuma kula da gidaje, ta wani fannin ma, don kara cimma burin wadatar wadannan kayayyaki, yayinda ake kakkafa garkuwar ganin sun rushe, saboda ambaliya da kuma fari.

A takaice, manyan ayyukan ruwan sha, suna da alaka, da wani manzali na wayewar kai, da kuma bunkasa da kuma faduwar manyan kasashe. Juyin halayyar aikin noman da suka kaddamar da wayewar kai, misalin shekaru dubu biyar, da suka wuce, sun ginu ne, a kan wata kwarewa, ta gagarumin aikin lambu, a yankunan dake doron kogunan dake Masar, dake tsohuwar daular Mesopotamia, da kuma Kurmin Indus. Tsohuwar daular Romawa, ta inganta yalwar wayewar kan mazauna birane miliya daya, a tsakiyar daular, dangane da kwararowar albarka, da kuma abubuwan da albarkatun ruwa ke kawowa, daga manyan magudanan ruwa, har goma sha ɗaya.

Tasowa da kuma muhimman gine-ginen shekaru arutan, a kasar China, su suka kammala babbar magudanar ruwan nan, mai tsawon mil dubu daya da 100 (misalin kilomita dubu daya da 770), wadda ta hade dukan albarkatun fadamar ta, da ake shuka shinkafa, a kudancin birnin Yangtze, wanda ke da yabanya, da busassar kasa, da kuma albarkatu, da ma kariyar duk wata kalubalen dake damun asar noman dake arewacin Kogin Yellow. Shi kuma lokacin daular Islama, ya samo asali ne, daga dadadden kasuwancin dukiyoyi, a fadin wuraren da suka gagari kutsawa, da yankin saharar da babu ruwa, amma, sai fadamu zuwa fadamun dake ajiye ruwan da fatake ke samun isasshen ruwan bai wa al'umma. Manya-manyan galmuna, da jigo, da ma makeken ruwan tekun da jirage ke zirga-zirga, suna yammacin farkon hanyoyin da suka shiga jagorancin sauran duniya ne. Muhimman kere-keren lokacin Juyin Harkokin Masana’antu, kamar shekaru 250 da suka wuce, sune na injin jirgin asan da James Watt ya kera. Canjin yanayin karuwar yawan jama’a, da kuma juyin yanayin rashin tsabta da kiwon lafiya, tun daga karshen karni na 19, har ya zuwa lokacin da aka yunkura kare cunkoso, a birane, da kuma rubanyar cututtukan da ake dauka, ta hanyar ruwa. Haka ma, kunno kan kasar Amirka, ya dauko alaka daga kwararewa da kuma hade wadansu muhallai uku, da suka bambanta da juna, a kan masaniyar harkokin ruwa: Yankinta, mai zafi, na rabin gabashin kasar, wanda ke da albarkar ruwan saman noma, da kuma kananan kogunan dake bayar da makamashi da kuma safarar masana’antu, da ma nasarar Kurden Erie, da ta taimaka wajen hadewarsu.

Dangantakar dake tsakanin zirga-zirgar jiragen ruwa, da mamayewar da gine-ginen Babban Kurden Panama ya yi wa fuskokin tekunta, biyu. Nasarar tunanin aka yi, a yankin da babu dausayi, na karshen yammacin Kasar, da ake noman ban ruwa, da samar da wutar lantarki, daga karfin ruwa, da kuma kulawa da ambaliyar da manya-manyan madatsun ruwan da shekarun fari suka taimaka ginawa, na Hoover ke haddasa. Yawaitar manyan madatsun ruwa, a fadin duniya, da kuma kasancewar daya daga cikin manyan makarraban dake tabbatar da Juyin Harkar Noman dake ciyar da linkin yawan jama’ar duniya, har sau hudu, a karni na 20, da kuma bullowar hadadden tattalin arzikin duniyar da ake da shi, a yau. Kowane shekara na da irin salonta, game da manyan matsalolin ruwa, a lokacinta. Kuma, har ya zuwa yau, irin haka na faruwa. Don ganin kuma an amince da cimma burin zamani, yana da muhimmanci, a kula da irin yadda muke da matukar bukatar tanadar matsayin rayuwarmu: alal misali, ta masu son cin nama, mai lagwada, dake cin fiye da ton uku, da digo bakwai, ko kuma lita dubu uku da 800, a kowane rana, ta hanyar ruwan da ake yin amfani da shi, wajen noman kayayyakin abinda ake ci. Wani fanni, daya, na yin tsiren gurasa, daga tsabar da ake bai wa dabbobi, ka]ai, na lashe kashi 60, cikin 100, na jimlar abinda ake ci. Wani fannin, daya, na audugar da ake saka kananan riguna, na bukatar lita dubu biyu da 850, da kuma ton biyu, da digo bakwai, kafin a girbe ta. Daga kuma malfar kirgin da ake yin takalma, da tufafin da kusan mafi yawan matsakaitan jama’ar kasar Amirka ke sanyawa, ana bukatar misalin ton 23, na ruwan da za a yi su. A wajen hada magungunan masana’antu, da na karafa, da na sarrafa kayayyakin abinci, da kuma hakar ma’adinai, ana kuma da bukatar ruwa, mai yawan gaske, wajen inganta yin harkokin kasuwanci. Idan har ana son a kera dan karamin sani sashe na abinda zai rika kai sakonni, a na’ura mai kwakwalwa, sai an bukaci, akalla, lita dubu bakwai da 600, ta gurbataccen ruwa mai nauyin ton bakwai da digo bakwai  idan kuma ana bukatar kera mota ce, to, ana bukatar kusan lita dubu 151, ko kuma ruwa mai nauyin ton 155.

A kasashen dake da arzikin masana’antu, mafi yawan ruwan, ana amfani da shi ne, ba a aikin noma ko samar da makamashi ba  fiye da kashi biyu, cikin   biyar na yawan ruwan daukacin kasar Amirka, yana tafiya ne wajen samar da makamashi da kuma, mafi yawan sanyaya injunan samar da wutar lantarki. Famfo, da safara da kuma tsabtace irin wannan dimbin ruwa — wanda yana kai nauyin kilo, a kowace lita, ko kuma nauyin kashi 20, cikin 100, na mai   na kaya daga cikin manyan matsalolin da ake samu, game da samar da makamashi da kuma ayyukan aikin injuna, dake fuskantar al’umma. Idan aka kamanta, a daukacin yankunan dake fama da rashin arziki, a duniya, inda ake da ‘yan bututun dake famfo da kai ruwa, da kuma wwahalar samar da ruwa mai tsabta, a kullum, mafi yawa, ta hanyar yin amfani da arfin dan adam.

Ayankunan karkarar kasar Kenya, inda na taimaka wajen hade bututun da babu ruwan a ciki, masu tsawon kilomita biyu, a wani kauye, a shekarar 2004, mata da kananan yara kan kai da komo, na tsawon awowi uku, a kowace rana, domin debo dan ruwan da ayyukan gida ke bukata misalin wanda zai wanke makewayi uku, ga mutum, amma, duk da haka, ba zai kai nauyin kilo 91 ba, ga gidan dake da iyalai biyar. A nan ake asarar yawan lokaci, da kuma hana yara zuwa makaranta, wadda wata alama ce, ta irin abubuwan dake karya zukata idan ma ana da bukatar ganin hakan kan irin yadda har ake da amfani da   gurbataccen ruwa, wajen harkokin bun}asa tattalin arziki.

Kalubalen Samar da Ruwa a Duniya[gyara sashe | gyara masomin]

Ana fama da irin yadda ake kara arangama da karancin ruwa, a duniya, domin muhalli, ko kuma mafitar harkokin siyasa. Bisa ga irin yadda ake jan ruwa, a ko’ina, fiye da yadda ake sake samar da shi, ta hanyar sabunta shi, da kuma yadda yake gurbacewa, a yanzu, da yadda bil adama ke kaskanta tsarin samar da ruwa mai tsabta, ya kai wani mummunan manzali. A sakamakon haka, a karo na farko, tun lokacin da wayewar kai ta zo, dole, mu san irin yadda za mu ri}a rarraba ruwan, domin tanadin harkokin kiwon lafiyar rashin gurbacewar muhallin da rijiyoyin al’umma ke kasancewa masu muhimmanci, ga harkokin tattalin arziki, da hidimar bil adama. Wata cikakkar kididdigar da Tsarin Tantance Shirin Tsabtace Muhalli, na Wannan karnin ya gudanar, game da harkokin kyautata tsabtar muhalli, a shekarar 2005, ya yi garga]i game da wannan al’amari. Ana ta kwalfar ruwa mai yawa, daga fiye da manyan koguna 70, ciki har da na Bahar Maliya, da Indus, da Yellow, da Euphrates da kuma Colorado, wadanda ambaliyar su ta daina kaiwa ya zuwa inda suke rarrabuwa, ko ma zuwa teku. Kusan rabin fadamun duniya sun bace. Daudar magungunan masana’antu, da gurbacewar da suka haifarwa, ba karamar illa ba ce, ga rayuwar kifaye, da gurbacewar ruwan sha, da ma wadda ke shiga cikin kayayyakin abincin bil adama. Daskararren ruwa, daga tsaunukan Himalayas, ya zuwa Andes, sai narkewa suke yi, fiye da yadda ake zato, a tarihin duniya, sai kuma kafewar da tushen wa]annan mala-malan kogunan ke yi, da kuma barazanar daidaituwar kasashen da suke dogara da ruwan kogunan. Kamar kuma yadda al’amarin rikice-rikicen muhallin ke kara dagulewa, haka mutuncin harkokin siyasa ke kara fallasuwa. A sama: Gazawar tabbacin rashin samun gangarowar ruwan da ake samu, a birnin Machu Picchu, ya sanya aka zayyana, da kuma shimfida tsohon garin nan, na Inca, dake kan tsaunin yankin. ©National Geographic Stock/Ralph Lee Hopkins[1]

Rarraba Dukiyar Albarkatun Ruwa[gyara sashe | gyara masomin]

Daya daga cikin manyan matsalolin dake damun shekarun karancin ruwa mai tsabta, ita ce yanayin kasashe na iya kasancewa mai rangwancin da za a iya raba fadamun koguna 263, da koramun }asa, da kuma dimbin daskararren ruwan dake ratsa kan iyakoki. Alal misali, kokarin kasar Iraq, na sake gina kasa, na fama da cikas, ta karancin wutar lantarki da ruwan aikin noman rani, bisa ga irin yadda kwararowar ruwan ke raguwa, ya zuwa Kogin Euphrates, wanda ake kada ruwansa zuwa kogunan kasashen Turkey da Syria. A bisa ga kiyasi, ayyukan ruwan wadannan kasashe uku, sun tahallaka ne, da samun kashi daya da rabi, na daukacin yawan ruwan dake kwararowa cikin kogin na Euphrates abinda kuma ke da wuya. Wadda ta fi amfana, watau kasar Turkey, ta na tsaka-tsaki ne, na kan yanke shawarar irin yawan abinda za ta bar wa kwadabtata Akwai ma irin hakan, dake neman faruwa, a Kudancin Asia, inda kasar China ta mamaye falalen yankin Tibet, daga daukacin dukan wani al’amarin dake da dangantaka da kogunan yankin, kan wadannan mutane miliyan dubu biyu, ke dogara da su.

A duk tarihi, mulki ya yi kaura zuwa saman koguna, tun lokacin da gwamnatoci suka samu galabar manyan harkokin fasahar da za su gudanar da kwararar ruwa. Irin wannan al’amarin ya fara kunno kai ne, a Kogin Bahar Maliya. A wannan karnin, gangaren asar ta Masar, ya fi shanye mafi yawan kason ruwan  kogin, duk da yake kashi 85, cikin 100, na ruwansa, sun faro ne, daga yankin da ya tagayyara, na kasar Habasha, wanda, har ya zuwa kwanan nan, ba ya amfana da komai daga irin ci gaban da ya samu. A cikin shekaru goma, da suka wuce, gwamnatocin kogin na Bahar Maliya, sun yi kokarin kulla yarjejeniyar bayar da hadin kan inganta kogin, da kuma rarraba ruwa, a yankin dake da matukar bukatarsa, da bunkasa kanana, da manyan ayyukan kusan kashi 50, cikin 100, na yawan mutane, miliyan dubu 500, nan da zuwa shekarar 2025. Tsohon Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya, Boutros Boutros-Ghali, wanda ka fi sani da hango hakan, kusan shekaru 25, da suka wuce, cewa duk wani yakin da za a yi, a karni na 21, ba zai wuce “yake-yaken da suka danganci na samar da ruwa ba.” Yayinda kasashe, a halin yanzu, suke gano karin dalilan da za su hada kai da juna, fiye da fadace-fadacen kan ruwa, sai hanzarta matsa lamba ake yi, kan irin yadda yawan jama’a ke karuwa, da kuma mugun karanci da hanzarta daidaita duk wata matsala game da canjin yanayi. Karancin ruwa, a kasashen dake ba su iya noma abincin da zai ishe su, da kuma makamashi da kayayyaki, sun fi fuskantar gazawa. Waɗannan gajiyayyun kasashen sun zama wuraren haifar da rashin zaman lafiya, da yake-yake, da kashe-kashen rayuka, da kuma ta’addancin duniya, da fashin kan ruwan teku, da annobar cututtuka, da fari, da dimbin gudun hijira, da ma sauran bala’o’in dake faruwa, a kan iyakoki.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://ng.usembassy.gov/wp-content/uploads/sites/177/ALAMARIN_RUWA_A_DUNIYA.pdf&ved=2ahUKEwjv7Y7ts-72AhWk_7sIHQJgCKYQFnoECAoQAQ&usg=AOvVaw06EPrkMed6r1GcpUx05y4e[permanent dead link]