Jump to content

Karatun Dijital

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Karatun dijital shine dagewan mutum don iya mu'amala da kuma sadar da bayanai ta amfani da dandali ko kafofin watsa labarai na dijital.  Duka wannan haɗin gwiwa ne na fasaha da fahimta wajen amfani da bayanai da fasahar sadarwa don ƙirƙira, ko raba bayanai.[1]

Yayin da ilimin dijital yafi maida hankali kan ƙarewa a fannin dijital da kwamfutoci masu zaman kansu, zuwan intanit  da kafofin sada zumunta ya karkata wasu daga cikin maida hankali ga na'urorin hannu watau (GSM). Hakazalika da sauran ma'anoni masu tasowa na ilimin karatu waɗanda ke gane hanyoyin al'adu da tarihi na samar da ma'ana, karatun dijital ba ya maye gurbin hanyoyin gargajiya na fassarar bayanai amma yana faɗaɗa ƙwarewar tushen waɗannan ilimin na gargajiya. Ya kamata a yi la'akari da ilimin dijital a matsayin wani ɓangare na hanyar samun ilimi.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://literacy.ala.org/digital-literacy/
  2. https://www.cambridge.org/core/books/digital-literacy-unpacked/EFCB8F14511A022ED1B4926797D443A1