Karl Toriola
| Rayuwa | |
|---|---|
| Sana'a | |
| Sana'a | business executive (en) |
Karl Olutokun Toriola shugaban kasuwanci ne na Najeriya. Shine Babban Jami'in Kamfanin na MTN Nigeria.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Toriola ya yi Digiri na farko a fannin Kimiyyar Lantarki da Wutar Lantarki daga Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, Najeriya sannan ya yi Digiri na biyu a fannin Kimiyyar Sadarwa daga Jami’ar Wales, Swansea, Birtaniya.
Ya yi aiki a Ericsson Nigeria a shekarar 2000 a matsayin Manajan Tallafi da Haɗin kai sannan ya koma Econet Nigeria a shekarar 2003 a matsayin mataimakin babban jami'in fasaha ya tashi ya zama babban jami'in gudanarwa a lokacin Vmobile Nigeria (yanzu Airtel). A shekara ta 2006 Toriola ya koma MTN Nigeria a matsayin babban jami'in fasaha, Shugaba MTN Kamaru a wannan shekarar. Ya ci gaba da zama mataimakin shugaban WECA na MTN Group (West and Central Africa) na tsawon shekaru 5 har sai da aka sanar da shi shugaban kamfanin na MTN Nigeria a watan Oktoba 2020.
Shi mamba ne na kungiyar Injiniya ta Najeriya, memba a Majalisar Dokokin Injiniya a Najeriya. da Cibiyar Gudanarwa. Yana kan Majalisar Mulki ta 12 a Jami’ar Jihar Legas, Nijeriya.
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Karl yana da aure kuma yana da ɗa daya tilo, Damilola Karla Toriola.