Kayan ƙwalliya na mata
Appearance

Kayan ƙwalliya na mata[1], kaya ne da mata musamman ƴan mata ke amfani dasu a jikin su domin ado da kwalliya da kuma burge mutane. kayan ƙwalliya an daɗe ana amfani dasu duk da kayan na sauyawa daga irin na wancan zamanin zuwan na wannan zamanin, a yanzun dai zamani ne da ƴan mata ke ƙure adakar su da kece raini ta hanyar ado da kayan ƙwalliya.
Amfanin kayan ƙwalliya
[gyara sashe | gyara masomin]- Tsabtace kai da jiki
- Farin jini a wajen mutane
- Kawo mijin aure ga ƴan mata
Illar kayan ƙwalliya
[gyara sashe | gyara masomin]- Suna haifar da illa ga fata
- Sauya lunin kalar mace
- Kawo ciwon kansa. Da dai sauran su[1]