Keshi Anderson
Keshi Stuart Oluyinka Adetokunboh Anderson (an haife shi a ranar 6 ga Afrilu 1995) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Ingila wanda kebuga kwallo a matsayin dan tsakiya da kuma ɗan wasan gaba na ƙungiyar Birmingham City.
Bayan ya buga wasan ƙwallon ƙafa na matasa tare da watford da kuma wasan ƙwallo wanda bana gasar kofi ba tare da Barton rovers , Anderson ya zama ƙwararren dan wasa lokacin yana tare da Crystal Palace a c 2015. Bai taba fitowa a cikin a tawagar farko ta Palace ba, kuma ya tafi aro a kungiyar doncaster rovers, Bolton Wanderers, Northampton Town da Swindon Town. Ya sanya hannu na dindindin ga Swindon a watan Janairun 2018, ya bar kulob din a watan Yunin 2020 don sanya hannu ga black pool.
Ayyukansa
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan ya kwashe lokaci tare da Kwalejin kwallon kafa ta, [1] Anderson ya fara babban aikinsa na kwallo tare da barton rovers, inda ya zira kwallaye 32 a wasanni 53 a dukkan wasanninsa, [2] ciki har da kwallaye 26 da yaci a gasanni. [3] ya taba zira kwallo a cikin minti shida yayin da yake kwallo a Brentford da Crystal Palace, kulob din na karshe ya sanya hannu a kansa a watan Fabrairun 2015. [4] Ya zira kwallaye a karon farko a kungiyar 'yankwallo na kasa da shekara 21, kuma kwana daya bayan haka manajan Palace Alan Pardew ya bayyana cewa Anderson zai kasance a cikin manyan' yan wasan sa don wasan da ke zuwa a Leicester City a ranar 7 ga Fabrairu. [5][6]
Anderson ya shiga kungiyar doncaster rovers a kan rancen wata daya a ranar 24 ga Satumba 2015 [7] kuma bayan yaje ya fara buga wasansa na farko da sheffield united bayan 'yan kwanaki. [8]A watan Oktoba, an tsawaita rancen har zuwa Janairun 2016.[9] A ranar 21 ga watan Nuwamba, Anderson ya karye kafa a wasan da ya yi da Rochdale wanda zai hana shi fita na watanni tara. [10][11]A ranar 31 ga watan Agustan shekara ta 2016, Anderson ya koma kungiyar Bolton Wanderers ta EFL League One a kan yarjejeniyar aro na tsawon lokaci.[12] Ya zira kwallaye a karon farko na Bolton lokacin da Wanderers suka zo daga baya suka yi 1-1 tare da Southend United a filin wasa na macron. [13] Crystal Palace sun sake kiran Anderson a ranar 16 ga watan Janairun 2017, kuma ya sanya hannu a kan Northampton Town a aro washegari. [14][15]
ranar 31 ga watan Agustan shekara ta 2017, Anderson ya koma kungiyar Swindon Town ta EFL League Two a kan aro har zuwa watan Janairun shekara ta 2018.[16] Kwanaki biyu bayan haka, ya fara bugawa Swindon a wasan da suka yi da barnet sukaci 4-1 a gida. Anderson ya sanya hannu a kungiyar blackpool a ranar 29 ga Yuni 2020 a kan kwangilar shekaru biyu, kulob din yanada zaɓi don tsawaita yarjejeniyar da ƙarin shekara guda.[17][18] Ya zira kwallaye na farko ga kulob din a wasan EFL Trophy da ya yi da Accrington Stanley a ranar 6 ga Oktoba 2020. [19]
A ranar 22 ga watan Yulin 2023, bayan jarabashi, Anderson ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara guda tare da kungiyar EFL Championship ta Birmingham City . [20][21] A ƙarshen kakar 2023-24, kulob din ya haifar da tsawaita kwangila.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Crystal Palace: Keshi Anderson's hat-trick that earned dream move". BBC Sport. 3 February 2015. Retrieved 4 September 2023.
- ↑ "Players: Keshi Anderson". Barton Rovers F.C. Archived from the original on 5 February 2015. Retrieved 7 February 2015.
- ↑ "Player profile: Keshi Anderson". Aylesbury United Archive. Luke Buckingham-Brown. Retrieved 4 September 2023.
- ↑ "Crystal Palace: Keshi Anderson's hat-trick that earned dream move". BBC Sport. 3 February 2015. Retrieved 4 September 2023.
- ↑ Muro, Giuseppe (4 February 2015). "Crystal Palace new-boy Keshi Anderson makes instant impact". London Evening Standard. Retrieved 7 February 2015.
- ↑ "Crystal Palace non-league signing Keshi Anderson in squad to face Leicester". The Guardian. Press Association. 5 February 2015. Retrieved 7 February 2015.
- ↑ "Keshi Anderson: Crystal Palace striker joins Doncaster Rovers". BBC Sport. 24 September 2015. Retrieved 24 September 2015.
- ↑ Samfuri:Soccerbase season
- ↑ "Loan Round Up". Crystal Palace F.C. 19 October 2015. Archived from the original on 26 October 2020. Retrieved 20 October 2015.
- ↑ "Doncaster Rovers 0 Rochdale 2: Anderson injury adds to Doncaster misery". Yorkshire Post. 23 November 2015. Retrieved 4 September 2023.
- ↑ "Anderson moves on loan to Bolton". Crystal Palace F.C. 31 August 2016. Retrieved 4 September 2023.
- ↑ "Anderson moves on loan to Bolton". Crystal Palace F.C. 31 August 2016. Retrieved 4 September 2023.
- ↑ Samfuri:Soccerbase season
- ↑ "Keshi Anderson returns to Crystal Palace". Bolton Wanderers F.C. 16 January 2017. Retrieved 4 September 2023.
- ↑ "Keshi Anderson: Crystal Palace striker joins Northampton Town on loan". BBC Sport. 17 January 2017. Retrieved 20 January 2017.
- ↑ "Breaking: Town Complete Deadline Day With Anderson Signing". Swindon Town F.C. 31 August 2017. Retrieved 1 September 2017.
- ↑ "Keshi Anderson Becomes Blackpool's First Summer Signing". Blackpool F.C. 29 June 2020. Archived from the original on 29 June 2020.
- ↑ "Blackpool: Keshi Anderson signs on two-year deal after Swindon Town release". BBC Sport. 29 June 2020. Retrieved 4 September 2023.
- ↑ Scrafton, Matt (6 October 2020). "Accrington Stanley (p) 1–1 Blackpool: Seasiders held to draw for second straight group game in EFL Trophy". Blackpool Gazette. Retrieved 4 September 2023.
- ↑ "Keshi Anderson signs for Birmingham City". Birmingham City F.C. 22 July 2023. Retrieved 22 July 2023.
- ↑ "Birmingham sign ex-Blackpool forward Anderson". BBC Sport. 22 July 2023. Retrieved 4 September 2023.