Kirsteen Mackay
Kirsteen Mackay ita yar Biritaniya ce kuma yar
Ostiraliya, wadda itace mai Gine-ginen Gwamnatin Australiya ta Kudu .
Ita ce mai rijistar gine-gine a cikin Burtaniya da Kudancin Ostiraliya.
Mackay ta yi karatun gine-gine a Makarantar Fasaha ta Glasgow kuma ta kammala karatun ta na digirinta na biyu fannin zane a Kwalejin Fasaha ta Royal da ke Landan. Ta na da gogewar shekaru 15 a cikin ayyukan sirri, irin su Marks Barfield Architects, kuma ta kasance tsohuwar shugabar Binciken Zane a Hukumar Gina Gine-gine da Muhalli ta Burtaniya (CABE) na tsawon shekaru hudu. Mackay ta kasance darekta na kamfanin gine-gine na Springett Mackay Architecture.
Ta kasance abokiyar aikin gine-ginen gwamnati a cikin Office for Design and Architecture SA (ODASA). A cikin Nuwamba shekara 2014 an nada ta Mukaddashin Architect na Gwamnati kuma Mukaddashin Manaja, Gine-gine da Gina Muhalli.
A cikin Yuli shekara 2015 an nada Mackay a matsayin mai Gine-ginen Gwamnatin Kudancin Ostiraliya. A cikin wannan rawar da ta taka ta jagoranci Cibiyar Gine-gine da Gina Muhalli na Sashen Tsare-tsare na Sufuri da Kayan Aiki na SA, tare da shirin Sake Tsara na SA.