Jump to content

Kogin Wainui (Manawatū-Whanganui)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Wani bangare na kogin
kogin wainui

Kogin Wainui kogi ne dake Tararua da yake gundumar Manawatū-WhanganuiTsibirin Arewa wanda yake yankin New Zealand. Ya tashi akan Mt McCartie kuma yana gudana kusan 28 kilometres (17 mi) kudu maso gabas ta hanyar keɓewar tsaunuka don isa bakin tekun Pacific a Herbertville, kilomita biyar yamma da Cape Turnagain. Sunan Wainui yana nufin manyan ruwaye. An samo shi daga kalmomin Maori wato wai ma'ana ruwa da nui ma'ana babba .

Kogin Wainui yana da ƙananan rafuffuka masu yawa.yankuna sun haɗa da (yamma zuwa gabas): Rafin Angora, Rafin Wimbledon, Rafin Waikopiro, Ramin Mangaone, Rafi na Mangaohau, Rafi Tapui, da Rafin Wairauka. [1] [2]

  • Jerin koguna na New Zealand
  1. New Zealand Topographic Map. Retrieved 8 January, 2020, from https://www.topomap.co.nz
  2. Map of Porangahau / Cape Turnagain. c1859. No author.