Ku Klux Klan
Ku Klux Klan | |
---|---|
| |
Bayanai | |
Iri | Tsarin Siyasa, hate group (en) , ƙungiyar ta'addanci, armed organization (en) da criminal organization (en) |
Ideology (en) | white nationalism (en) , Christian terrorism (en) , nativism (en) , anti-Catholicism (en) , anti-communism (en) , neo-fascism (en) da white supremacy (en) |
Subdivisions | |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1865 |
Wanda ya samar |
Nathan Bedford Forrest (mul) |
Founded in | Pulaski (en) |
Ta biyo baya | Knights of the Ku Klux Klan (en) |
kkk.bz |
Ku Klux Klan wanda ake gajartawa kamar haka: KKK or the Klan, wani kungiya masu tsatssaurar ra'ayi ne mabiya kiristanci furotentant, masu daukaka fararen fata, kungiyar masu kiyayya da mutane, masu ta'addanci ga mutane. An kirkire ta a shekarar 1865, a lokacin sake fasali barnar yaki na Kudu. Da yawa daga cikin masana tarihi sun alakanta kungiyar Klan a matsayin kungiyar ta'addanci na farko a Amurka.[1][2][3][4] Kungiyar ta kunshi kungiyoyi daban daban wanda aka tsara a matsayin kungiyoyin asiri, wadanda mafi yawan lokuta sun aiwatar ayyukan ta'addanci, tashe-tashen hankula, da kuma ayyukan tsoratarwa don tursasa tsarinsu da kuma hantarar wanda suka cutar, mafi akasari daga Afirkawan Amurka, Yahudawa, Kiristocin katolika. An samu bayyanarsu sau uku a lokuta daban-daban da dumbin manufofinsu dangane da wuri da lokaci.
Kowanne bayyana na kungiyar Klan yazo ba tare da hauhawar wasu lokutan wanzuwa ba, wanda ya hada da sassan gargajiya da yawa tare da karancin ko kuma rashin tsayayyen manufa. Dukkansu sun yi fafutukar hakkin ra'ayoyin siyasa kamar daukaka fararen fata a kasa, adawa da karbar 'yan gudun hijira ko baki,—da kuma musamman a sababbin kungiyoyi— kiyayya ga kabilar Nordic, kiyayyar Yahudawa, kiyayya ga mabiya Katolika, kiyayya ga 'yan madigo da luwadi, daukaka hakkin 'yan asalin kasa, kiyayya ga Kwaminisanci, adawa ta masu da'awar babu Allah, da kuma adawa da mabiya addinin Islama. Klan na farko, wanda tsofaffin sojojin Confederate suka kafa, sun kai hari kuma sun kashe masu karfin ikon siyasa Bakaken fata da kuma fararen fata da suke mara masu baya a Kudancin Amurka.[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Fergus Bordewich. (2023). Klan War: Ulysses S Grant and the Battle to Save Reconstruction. Penguin Random House
- ↑ "The Untold Story of Grant vs. the KKK: A Deep Dive with Historian Fergus M. Bordewich". YouTube. November 17, 2023. Retrieved November 17, 2023.
- ↑ Bullard, Sara (1998). The Ku Klux Klan: A History of Racism and Violence. DIANE Publishing. p. 6. ISBN 978-0-7881-7031-7. Retrieved August 1, 2024.
one of the nation's first terrorist groups
- ↑ Jacobs, David; O'Donnell, Patrick (2006). Ku Klux Klan: America's First Terrorists Exposed : the Rebirth of the Strange Society of Blood and Death. 8: Idea Men Productions.
Historians have suggested a combination of reasons for the eventual decline of the Ku Klux Klan of the Reconstruction period: 1)growth of public sentiment in the South against activities of masked terrorists
CS1 maint: location (link) - ↑ "Ku Klux Klan Established". Civil War on the Western Border: The Missouri-Kansas Conflict, 1855–1865. Digital History, Kansas City Public Library. Archived from the original on January 26, 2023. Retrieved January 26, 2023.