Kubra Noorzai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kubra Noorzai
Rayuwa
Haihuwa Kabul, 1932
Mutuwa 1989
Karatu
Makaranta University of Paris (en) Fassara
Sana'a
Sana'a civil servant (en) Fassara

Kubra Noorzai haihuwa (1932-mutuwa 1986) ta kasance'yar siyasan Afganistan ce. Ita ce mace ta farko da ta zama ministar gwamnati a kasar,[1] tana aiki a matsayin Ministar Kiwon Lafiyar Jama'a tsakanin shekarar alif dari tara da sittin da biyar 1965 zuwa alif dari tara da sittin da tara 1969.

Tarihin rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Noorzai a Kabul, daya daga cikin yara tara.Ta yi karatu a Lycée Malalaï, kafin ta kammala digiri a Kwalejin Kimiyya a Jami'ar Kabul.[2][3]Daga baya Noorzai ta koma Lycée Malalaï, inda ta zama shugabar ta kuma daga baya ta jagoranci tsangayar mata a jami'ar Kabul. [3]A shekarar 1958 ta koma Faransa, inda ta yi karatu a Jami'ar Paris na shekara guda.[2] [3]Ta yi aiki a matsayin mai duba makaranta na makarantun 'yan mata, [4] kuma ta yi aiki a matsayin darekta na Cibiyar Agaji ta Mata a Kabul. [5]Ta kuma zama shugabar kwalejin tattalin arzikin gida.[6]

Daya daga cikin jagororin masu rajin kare hakkin mata a Afganistan, Noorzai na daya daga cikin matan farko da suka daina sanya mayafi a bainar jama'a, bayan Sarauniya Humaira Begum ta ba da misali da fitowa ba tare da nata ba a shekarar 1959.[4]Ta kasance wakiliyar Afghanistan a UNESCO da taron Majalisar Mata ta Duniya a Dublin. [2]A cikin shekarar 1964, Sarki Mohammed Zahir Shah ya nada ta a cikin kwamitin ba da shawara wanda ya sake duba daftarin tsarin mulkin a shekarar 1964, [7] wanda ya bai wa mata 'yancin kada kuri'a da tsayawa zabe.Bayan zaben watan Agusta-Satumba a shekarar 1965, Firayim Minista Mohammad Hashim Maiwandwal ya nada ta Ministar Kiwon Lafiyar Jama'a a ranar 1 ga watan Disamba shekarar 1965,[8] ta zama ministar mata ta farko a Afghanistan.Ta kasance a ofishin har zuwa shekarar 1969.[9]

A matsayin darektar Cibiyar Mata, an zabe ta a Loya Jirga a shekarar 1977, a lokacin mulkin Shugaba Mohammed Daoud Khan.[10]

Ba ta taɓa yin aure ba, ta mutu a gidanta da ke unguwar Kārte Seh a birnin Kabul a shekara ta 1986. [3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. George Grassmuck, Ludwig W. Adamec & Frances H. Irwin (1969) Afghanistan, Some New Approaches, p319
  2. 2.0 2.1 2.2 Lucie Street (1967) The Tent Pegs of Heaven: A Journey Through Afghanistan, p168
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 Kubra Nurzai, 1932-1986, 1st Woman Minister of Afghanistan Abarzanan
  4. 4.0 4.1 Tamim Ansary (2012) Games without Rules: The Often-Interrupted History of Afghanistan
  5. Information Bulletin 1960 - Library of Congress, p627
  6. The Kabul Times Annual, Volume 1, p15
  7. Sarfraz Khan (2013) Politics of policy and legislation affectin g women in Afghanistan: One step forward two steps back[permanent dead link] Central Asia Journal, Number 73
  8. Breaks Barrier Sarasota Herald-Tribune, 2 December 1965
  9. Rosemarie Skaine (2010) The Women of Afghanistan Under the Taliban
  10. Suad Joseph & Afsāna Naǧmābādī (2003) Encyclopedia of Women and Islamic Cultures: Family, Law and Politics] p788