Kunun Aduwa
Appearance

Kunun Aduwa
[gyara sashe | gyara masomin]Aduwa dai wata bishiya ce mai ƴaƴa wacce takeda ƙayoyi dayawa ajikin ta, wasu ma suna kiranta da bishiyar ƙaya. Ƴaƴan Aduwa suna da zaƙi idan suka nuna, amma akwai wasu masu daci daga cikin ƴaƴan Aduwa.[1]

Yanda ake kunun aduwa
[gyara sashe | gyara masomin]Idan an wanke aduwar sai a jiƙa ta aruwa ta kwana kamar biyu zuwa uku, zata jika sosai.
Sannan za'a cire kwallayen Aduwar ayayinda tanarke acikin ruwan.
Sai asamu garin gero, da gyaɗa, sai a zuba a blander ko injin markaɗe amarkaɗa aguri guda.
Bayan an tafasa ruwa sai azuba akan kamun nasu.
Nan take zai koma kunun aduwa.
Idan Kuma yayi sanyi
Zaiyi tauri ne kamar Gaya.