Kweku Boateng-Lovinger

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kweku Boateng-Lovinger
Member of the 2nd Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 1997 - 6 ga Janairu, 2001
District: Birim North District
Election: 1996 Ghanaian general election (en) Fassara
Rayuwa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Kweku Boateng-Lovinger ɗan siyasan Ghana ne kuma ɗan majalisa na biyu na jamhuriya ta huɗu mai wakiltar mazabar Brim North a yankin Gabashin Ghana.[1]

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Kweku a Brim North a Gabashin kasar Ghana.[2]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

An fara zaben Kweku a matsayin dan majalisa akan tikitin jam'iyyar National Democratic Congress na mazabar Brim North a Gabashin Ghana a lokacin babban zaben Ghana na Disamba 1996. Ya samu kuri'u 20,737 daga cikin 44,630 masu inganci da aka kada wanda ke wakiltar kashi 36.00% a kan abokin hamayyarsa Owusu Agyekum na jam'iyyar Convention People's Party wanda ya samu kuri'u 12,139 da ke wakiltar 21.10%, Victor Biscoff Owusu Ahinkorah na New Patriotic Party, wanda ya samu kuri'u 6111. Boateng wanda ya samu kuri'u 448 da ke wakiltar kashi 0.80% da Alex Oduro-Ampadu wanda ya samu kuri'u 0. Ya yi rashin nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyarsa a hannun Grace Omaboe.[3][4][5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Ghanaian Parliamentary Register(1993-1996)
  2. Ghanaian Parliamentary Register(1993-1996)
  3. Ghanaian Parliamentary Register(1993-1996)
  4. FM, Peace. "Parliament - Birim North Constituency Election 1996 Results". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-10-12.
  5. FM, Peace. "Parliament - Birim North Constituency Election 2000 Results". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-10-12.