Lacumazes
Lacumazes | |
---|---|
Rayuwa | |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Oezalces |
Ahali | Capussa |
Sana'a |
Lacumazes sarki ne na tsohuwar kabilar Numidian Massylii a shekarar 206 BCH.
Tarihin rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Lacumazes shi ne ƙaramin ɗan Oezalces, ɗan'uwansa shi ne Capussa. Yayinda yake matashi, an dora shii a kujerar mulki ta Massylii ta hanyar shugaban Numidian, Mazaetullus, wanda ya tsige shi daga kan karagar kuma ya kashe Capussa.[1][2] A lokacin da Masinissa ya koma Afirka, Lacumazes ya tsere ya nemi mafaka a kotun Syphax don neman taimako; amma kafin ya isa inda yake, Massinissa ya kai masa hari, kuma ya tsere wa kama shi. Daga Syphax ya sami dakarun taimako, tare da wanda ya haɗu da mai kula da shi, Mazaetullus, kuma ya fuskanci Massinissa, amma an ci sojojin biyun da yaki. Lacumazes da Mazaetullus sun tsere kuma sun nemi mafaka a kotun Syphax. Massinissa ya ƙarfafa shi ya dawo kuma an karbe shi a kotun Massylii tare da duk girmamawa saboda jininsa na sarauta.[3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Lua error a Module:Citation/CS1/Utilities, layi na 129: Called with an undefined error condition: invalid_param_val.
- ↑ Fage, J. D.; Oliver, Roland Anthony (1975). The Cambridge History of Africa (in Turanci). 2. Cambridge University Press. p. 180. ISBN 9780521215923.
- ↑ Smith, Sir William (1846). Dictionary of Greek and Roman Biography and Mythology (in Turanci). 1. p. 703.