Jump to content

Ladi Tublees

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Ladi Tublees

Shahararriya jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud, ta Dade tana fim , fitacciya ce tana taka rawa a matsayin uwa a masana'antar.[1]

Takaitaccen Tarihin ta

[gyara sashe | gyara masomin]

[2]Ladi Tublees jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa, ta Dade tana fim ,tayi fina finai da dama a masana'antar, Cikakken sunan ta shine Ladidi Abdullahi anfi sanin ta da Tublees, Haifaaffiyar jihar kaduna ce a unguwan sabon garin nasarawa,tagi karatun firamare da sakandiri a garin kaduna,daga Nan Bata cigaba ba Akai mata aure, Amma auren be jima ba suka rabu da mijin,daga Nan ta sayi form din Aikin sojan ruwa ,sunan ta yafito tayi komai SE Allah be nufa tayi aikin ba.wata Rana SE Rabi'u rikadawa yace tazo tayi fim, SE Taki Yi, wataran suna hira da Zainab Abubakar tace nazo muyi Wani fim ,duk randa za,a fara fim din zata kirani,da za,a fara ta kirani naje Alfa care,yaga yadda take acting ya Yaba ,daga Nan aka dinga SATA a drama tana Yi kasance war tayi a makarantar su,daga Nan tai Wani fim da rikadawa,daga Nan nasiru gwagwazo zeyi fim Mai suna balarabe na Balaraba ya kirata tazo tayi fim din,fim din data fara na turanci ne Mai suna Alfa care.

  1. https://hausa.legit.ng/1163388-dandalin-kannywood-babu-macen-da-ta-kai-yar-fim-dadin-aure-jaruma-ladidi-tubeless.html
  2. https://www.hausaloaded.com/2018/04/taaitaccen-tarihin-ladidi-tubless.html