Lantarki
|
Wikimedia disambiguation page (en) |




Lantarki wannan kalmar na nufin samar da wuta don amfani ko walwala. Ita wutar lantarki tana da mahimmanci a rayuwa musamman a birni, ita lantarki ita take samar da wuta wacce ake amfani dashi.[1]
Ana samar da wutan lantarki ta hanyoyi mabambanta kamar ta hanyar Dam (hydropower), hasken rana, makamashin nuclear ko kuma ta hanyar iskan guguwa da dai sauransu.[2][3]
Mafi sauki cikin wadannan hanyoyin shi ne hanyar amfani da hasken rana.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]Yan Najeriya na ci gaba da shafe ranaku da dararensu a lokuta daban-daban ba tare da wutar lantarki ba na tsawon kwanaki sakamakon lalacewar babban layin lantarki na ƙasa da ake kira National Grid a turance. Da ma dai ɗaukewar lantarki ba sabon abu ba ne a Najeriya, yayin da layin lantarkin ya lalace sau da yawa a cikin shekarar nan. A ranar Lahadi da ta gabata, kamfanonin da ke raba lantarkin ga kwastomominsu suka tura wa 'yan Najeriya da dama irin wannan saƙon cikin harshen Ingilishi: "Gare ku abokan hulɗarmu masu daraja, muna masu baƙin cikin sanar da ku lalacewar layin wuta babban layin lantarki na ƙasa [National Grid]. "Wannan ya shafi dukkan ayyukanmu na ƙoƙarin biyan buƙatunku da kyau. Muna roƙunku afuwarku yayin da muke ci gaba da aikin haɗin gwiwa da [kamfanin rarraba lantarki] TCN don shawo kan matsalar." Ƙarshen makon da ya gabatan ya zama karo na kusan shida da babban layin lantarkin ke samun matsala cikin wata biyu. A wannan maƙalar za mu yi duba ne kan Mene ne National Grid? Me ya sa yake lalacewa? Ta yaya ake tarawa da rarraba lantarkin?[4]
Wanda aka fi karantawa Babban layin wutar lantarki na Najeriya - power grid a Turance - gungun layuka ne da suka haɗa tashoshin samar da lantarki da ke bai wa dukkan sassan Najeriya wuta. A taƙaice, wata ma'dana ce da ke ɗauke da dukkan lantarkin da ake sha a Najeriya. Haka nan, ba wani wuri ba ne guda ɗaya, tarin layuka ne a wurare daban-daban. An tsara shi ne don ya yi aiki ta wasu taƙaitattun hanyoyi musamman dangane da yawan wutar da ake da ita, da tsaron lafiyarsa. Saboda haka duk sanda ya fita daga yanayin da ya saba zama na kwanciyar hankali, ayyukan da yake za su samu matsala kuma hakan kan sa ya lalace. Na'urorin da ke ba da wutar lantarkin kan kashe kansu da zarar sun fuskanci cewa suna cikin matsala. Hakan ka iya nufin ɗaukewar wutar gaba ɗaya ko kuma na wani ɓangare. Kazalika, yanayi - iska ko ruwa ko sanyi ko zafi - kan shafi aikin babban layin a wasu lokuta, abin da ya sa ke nan ake yawan ɗauke wuta idan aka fara iska mai ƙarfi a lokuta da dama.[5]
- ↑ Hornby, A s (2000). Oxford Advanced learner's Dictionary of Current English (8 ed.). Oxford University Press. ISBN 9780194799126.
- ↑ https://ha.m.wiktionary.org/wiki/lantarki
- ↑ https://bakandamiya.com/lantarki/
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc