Lindiwe Chibi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lindiwe Chibi
Rayuwa
Haihuwa Afirka ta kudu, 1976
Mutuwa 2007
Sana'a
Sana'a Jarumi da ɗan wasan kwaikwayo

Lindiwe Chibi (1976–2007), ƴar wasan kwaikwayo ce ta Afirka ta Kudu. Ana yi mata kallon ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan kwaikwayo a gidan talabijin na Afirka ta Kudu, an fi saninta dalilin rawar da ta taka a matsayin 'Doobsie' a cikin fitaccen fim ɗin Muvhango.

Harbin bindiga da Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 30 ga watan Afrilu 2005, saurayinta Dan Mokoena, ya harbe ta a fuska lokacin da Chibi ke gidan mahaifiyarta.[1] Harbin da aka harba a kusa, ya shiga kumatu kuma ya fita ta bayan kanta. Cikin gaggawa an Kaita asibitin Garden City Clinic ta kasance acan na ɗan makonni. Bayan tashi daga coma, ta gurgunta a gefen dama na jikinta. lokacin da ta warke daga mummunan rauni, ta mutu daga cutar huhu a asibitin Chris Hani-Baragwanath da ke Soweto a 2007 tana da shekaru 31 a duniya.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "'Doobsie' written out of soapie". news24. Retrieved 2020-11-30.
  2. "Throwback: South African soap stars who died in real life". all4women. Retrieved 2020-11-30.

Hanyoyin Hadi na waje[gyara sashe | gyara masomin]