Lois Auta
Lois Auta | |
---|---|
Lois Auta | |
Haihuwa |
Jos, Nigeria | 29 Afrilu 1980
Wasu sunaye | Nbwuat'ayan |
Aiki | activist |
Shahara akan | Rights of persons living with disabilities |
Title | Chief executive officer |
Uwar gida(s) | Mr Innocent |
Yanar gizo |
cedarseedfoundation |
Lois Auta (an haife ta ranar 29 ga watan Afrilu a shekarar 1980) ita ce ta assasa kuma ta kasance shugaban Gidauniyar Cedar Seed, kungiyar da ke bunkasa tarayyan mata masu nakasa a tafiyan ci gaban kare haƙƙin ɗan adam a Najeriya. Tana mai da hankali kan dokokin da suka hada da mutane masu nakasa.[1]
A cikin shekarar 2019, Auta ta yi takara a matsayin AMAC (Majalisar Yankin Abuja)/ Majalisar Dokoki ta Kasa na Bwari, a 2022 [2] ta nemi kujerar Kaduna State House of Assembly don wakiltar mazabar Kaura a ƙarƙashin dandalin jam'iyar All Progressives Congress wato (APC) amma ba ta samu nasaran lashe zaben ba inda ta fiskanci faduwA a zaben fidda gwani ga Nehemiah Sunday. Ta fuskanci nuna bambanci a matsayin miskiniyyar mace 'yar siyasa.[3][4]
Rayuwa ta farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Auta a garin Jos Plateau, Jihar Plateau dake Arewacin Najeriya a ranar 29 ga Afrilu 1980 a cikin zuriyan Auta Akok na Kukum Gida Kagoro.
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Yayinda take yarinya, Auta ta kamu da cutar shan inna kuma an tsare ta a kan keken guragu. Tana da takardar difloma da digiri na farko a bangaren Gudanarwar Gwamnati daga Jami'ar Abuja, Najeriya . Ta yi karatun gudanar da harkokin kasuwanci na duniya a Jami'ar Nexford, da ke Washington, DC.
A cikin shekarar 2014, Auta ta shiga cikin Matasan Shugabannin Afirka kuma an zabe ta a matsayin abokiyar koyo na Mandela Washington [5]
Matsayi
[gyara sashe | gyara masomin]- Auta ta kasance wacce ta assasa kuma babban darakta na Cedar Seed Foundation.
- Shugaban kungiyar wasanni masu nakasa dake FCT, Abuja
- Memba na kwamitin Tarayyar Ma'aikatan Jama'a Ma'aikatan da ke da nakasa da yawa
- Mataimakin Mai Gudanar da Ƙasa na Advocacy for Women with Disabilities Initiative
- Memba na kwamitin Potters Gallery Initiative
- Memba na Ƙungiyar Ƙasashen Mutane masu nakasa
- Ta assasa Ability Africa
- Shugaba na Women on Wheels Multipurpose Cooperative Society
- Mataimakin shugaban kungiyar Mandela Washington Fellowship Alumni Association,Najeriya
A 2019, Auta ta nemi kujerar AMAC (Majalisar Yankin Abuja) / Bwari kujerar Majalisar Dokokin Kasa ta Babban Tarayya, kuma a cikin 2022, ta nemi samun kujerar majalisar dokokin Jihar Kaduna don wakiltar mazabar Kaura a ƙarƙashin dandalin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), amma ba ta rasa samu nasaran lashe zaben fidda gwani zuwa Nehemiah Sunday.[6] Ta fuskanci bambantaka kasancewa ta 'yar siyasa mace mai nakasa.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "President Buhari to host tech's brightest minds at Aso Rock". Nigerian Newspaper Toda. Retrieved 29 September 2016.
- ↑ Rapheal (2022-07-04). "Road to 2023: Why APC'll win 2023 poll –Lois Auta, founder of Cedar Seed Foundation". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-02-16.
- ↑ Ukwu, Jerrywright (2019-02-10). "Meet Lois Auta, a physically-challenged woman running for office in Abuja". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Archived from the original on 2020-08-11. Retrieved 2021-03-13.
- ↑ "From where I stand: "Disability will not stop me from achieving my dreams."". UN Women (in Turanci). 6 February 2019. Retrieved 2021-03-13.
- ↑ "Biographies-of-the-2014-mandela-washington-fellows". YALI. Retrieved 13 September 2022.[permanent dead link]
- ↑ Rapheal (2022-07-04). "Road to 2023: Why APC'll win 2023 poll –Lois Auta, founder of Cedar Seed Foundation". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-02-16.
- CS1 Turanci-language sources (en)
- All articles with dead external links
- Articles with dead external links from September 2024
- Articles with invalid date parameter in template
- Articles with permanently dead external links
- Articles with dead external links from March 2019
- Rayayyun mutane
- Haihuwan 1980
- Mutanen Kudancin Kaduna
- Mutanen Najeriya masu nakasa