Jump to content

Lokutan shekara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

lokaci Wani abu ne da Allah ya tsara shi bisa ka'ida da kuma yanayi,duk wata halitta ta da Ubangiji yayi to akwai irin yanayin da take rayuwa a ciki,a haka Allah ya tsara rayuwar mu domin mu rayu a ciki.

Ubangiji ya tsara duniyar nan bisa lokaci,kuma akwai lokacin da zata ƙare,a haka Ubangiji yake son yaga duk dan'adam.

A nahiyar Afirka akwai ire-iren yanayi da Ubangiji ya tsara kamar a bangaren Nigeriya akwai yanayi kala uku kamar yankin arewacin Najeriya.

Yanayin lokutan shekara

[gyara sashe | gyara masomin]

Kamar: lokaci na Rani, lokaci na [[Damina]], lokaci na kaka.

Lokacin Rani

[gyara sashe | gyara masomin]

Lokaci ne da al'umma karkara suke tafiye-tafiye barikin domin neman kudi, awannan lokaci duk wanda ka gani ya zauna a ƙauye to akwai abin da yakeyi kama daga kiwo ko noman [[Rafi]]yakan daƙile shi wajen fita bariki, mutanen ƙauye suna fita maƙwaftan jahohin su, su nema na kan su.

Lokacin Damina

[gyara sashe | gyara masomin]

A wannan lokaci Duk me himma daya tafi neman kudi a bariki ya kan dawo gida domin yayi aikin noma,sannan ya kanyi tanadi irin su:taki,abokan ƙwadago su taya shi aiki

Lokacin kaka

[gyara sashe | gyara masomin]

Da zaran ruwa ya dauke to dukkan hankali Manomi ya kan koma gona domin yayi girbi kayan da aka noma,shi dai manomi ya kanyi alfahari da wannan lokaci musamman ma idan ya samu amfanin gona da yawa,daga bisa Ni a kawo kayan hatsin da aka girbe gida, mutanen karkara su kanyi tanadin auren ƴaƴan su a irin wannan lokaci.