Jump to content

Lomasontfo Dludlu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lomasontfo Dludlu
Rayuwa
Haihuwa 1947
ƙasa Eswatini
Mutuwa 10 ga Janairu, 2011
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Mamba Parliament of Eswatini (en) Fassara

Lomasontfo Martha Dludlu (ta mutu ranar 10 ga watan Janairun 2011) 'yar siyasar kasar Swazi ce. A shekara ta 1993 ta zama mace ta farko da aka zaba a Majalisar dokoki a kasar.

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Dludlu ta girma a cikin karkara ba ts sami ilimi na yau da kullun ba.[1] Ta yi aiki a matsayin mai karfafa al'umma kuma ta kula da mazaunan yankin da suka hada da nakasassu da marayu.[1]

Duk da cewa ba ta iya karatu da rubutu ba, [1] ta tsaya takara a babban zaben shekarar 1993 a Maphalaleni kuma an zabe ta a Majalisar Dokoki, inda ta doke maza takwas da wata mace, ta zama mace ta farko da aka zaba a Majalisar.[2] Ta kasance memba a majalisar har zuwa shekarar 1998.[1]

Ta yi fama da bugun jini a shekarar 2008 daga baya ta mutu a gidanta a ranar 10 ga watan Janairun shekara ta 2011 tana da shekaru 64' aduniya.[2]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 Toolkit for Gender Sensitive Electoral Education Women and Law Southern Africa
  2. 2.0 2.1 First woman MP passes on Times of Swaziland, 13 January 2011