Jump to content

Ma adanai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Cigaban kowace al'umma ya ta allaka ne da iya adadin yadda zasu iya sarrafa ma'adanan su, ta samar da ingantaciyar rayuwa. ma'adanai wasu abubuwane da suke boye acikin kasa, ruwa,duwatsu har ma acikin tsaunuka, Wanda akan tone su domin bunkasa tattalin arziki da kuma kasuwancin kasa gami da amfanin al'ummar wannan kasar. Wanda kuma aturance bature na kiransu da (Natural resources)[1].

Ma'adai wasu abubuwa ne da ake samun su a kar kashin kasa, dutsi, da kuma kasan ruwa ta hanyar tonowa, fasawa da dai sauransu,.kamar irin su zinare, lu'ulu man fetur, farar -kasa da dai sauransu.

Akan iya cewa kowace kasa ta alaka da ma adanai ta fani tattalin arziki da cigaba kasa gami da anfanin wurin kasa wurin tafiyar da harkokin yau da kullum.

IRE -IREN MA'DANAI

[gyara sashe | gyara masomin]

ma' adamai sun kasu gida hudu

1-Ma'adanan kasan ruwa

2- Ma'adanan kasa

3- Ma'adanan cikin iska

4- Ma'adanan rana

MA'ADANAN KASAN RUWA

[gyara sashe | gyara masomin]

Ma adanan kasan ruwa wasu nau'in abubuwa ne da ake samu a karkashin ruwa ,Wanda ya hada da teku,kogi kai harma da koramu , kamar su lu'u-lu'u, zinare da dai sauransu ,wasu ma'adanan akan samesu ne a ruwa kuma akan iya samun irinsu a cikin kasa.

Ana tono wa'innan ma'adanan ta hanyar Gina bango don hana ruwan gudu,wasu kuma akan tonosu ne ta hanyar anfani da na'urori da kuma inginan zamani.

MA'ADANAN KASA

[gyara sashe | gyara masomin]

Ma'adanan cikin kasa suma nau'ine na abuwan da ake samu akar kashin kasa ,misali Danyan mai Wanda bature kema lakani da (crude oil) ,Uranium farar kasa ,Dutsin karfe Wanda bature kewa lakani da( Iron -Ore) da dai sauransu, mafi yawancin ma adanan anfi samun su ne akasa .

MA'ADANAN CIKIN ISKA

[gyara sashe | gyara masomin]

Ma'adanan cikin iska wasu nau in ma adanan ne da suke acinkin iska Wanda sun hada da iskar Nitrogen gas,iskar carbon da dai sauransu,ma'dan iska za a iyya cewa angano su ne daga baya ta hanyar anfani da injina da fassaha ta zamani.[2]

MA'ADANAN RANA

[gyara sashe | gyara masomin]

Ma'adanan rana nau in ma adanai ne da ake samu sakamakon haske ,Wanda ake anfani da fassahar zamani da sarafa wannan ma adanan wajen daga nau in haske zuwa wani nau in wurin samar da wutar lantarki da sauransu

Anfanin ma adanan Nada yasa Wanda ya had da da kasuwanci Dan karfafa tattalin arkin kasa ,samar da yawaita na abubuwan anfani na yau da kullum ,ta fanin suffuri,kere-kere na injinan zamani na kuma gine -gine.

Ma'adanai a kullum sune gaba wajen cigaban tattalin arziki na kowace alumma ,iya sarafa ma adanai daga wani nau'i zuwa wani nau'in a yayinda tabbatar da cigaban wannan kasa ta hanyar ilimin kimiya da fassaha, dole ne sai da ilimin kimiya sannan akan iya tono ko samar da wasu Ma'adanan musamman Ma'adanan da iska, Wanda ba a ganinsu da idanu [3].


  1. Littafin fassaha (comprehensive geography)
  2. Litaffin kundin ilimi
  3. Shafin internet na wikipedia