Majalisar Malaman Afrika

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Majalisar Malaman Afrika

Majalisar Malaman Afrika majalissar malamai ce dake nahiyar Afirka a kudancin sahara.

Asali[gyara sashe | gyara masomin]

Tunanin kafa wannan Majalisa ta malaman Afrika, wadda take kudancin sahara,duk lokacin da aka haɗu a wuraren taruka da sauran hidimomi, irin wadanda malaman Afrika kan halarta tare da bayar da tasu gudunmawa. Sawa’un waxannan taruka, irin waxanda ake shiryawa ne tare da kuma gudanarwa a cikin wannan yanki na Afrika ko a wajensa. Kai har aka wayi gari wannan tunani ya zama wani abin tattaunawa da tsokaci a tsakanin malaman wannan nahiya, ta hanyar musayar saqonni irin na kar-ta-kwana ta hanyar kafafen sadarwa na zamani. A haka kuma har aka gamsu da cewa, lokaci fa ya yi, wanda kuma ya kamata a cikinsa, a fito da wannan tunani a fili kuma a aikace. Musamman, saboda ganin irin yadda sabbin abubuwa da dama, suke ta kara faruwa kuma a cikin gaggawa a duniyarmu ta yau,  mai cike da qungiyoyi da majalisu barkatai, farare da baqaqe.

Abin da yake tafe a cikin wannan takarda, wani xan taqaitaccen tarihi ne na wannan Majalisa, da irin yadda aka shimfixa tare da kafa ta tun farko har zuwa yau.[1].

Manufa[gyara sashe | gyara masomin]

An yi tunanin kafa wannan Majalisa ne a kan tunani, da manufar ta zama wani qasaitaccen zaure ga malaman wannan yanki na duniyar Afirka da ke kudancin sahara, wanda zai zama wata makoma ta ilimi da neman fatawa, tare da yin gagarumin tasiri a tsakanin gaba dayan al’umomin Afrika. Wata manufar kuma ita ce, inganta matsayi da irin gudunmawar da malamai masu wa’azi suke bayarwa, a wayi gari sun zama jagoran rayuwa  ga gaba dayan al’umomi da ma qabilu da suke rayuwa a wannan yanki, ta hanyar samarwa fatawa cikakken tsari da kangado. Burin wannan Majalisa ne, ta riqa tsoma baki a cikin al’amurra da matsalolin rayuwar jama’ar wannan yanki, ta gaba daya. Sa’annan kuma ta zama ita ce ke magana da yawun bakin musulman wannan yanki na Afrika,dama daukacin tarukan cikin gida, da na waje, da ma matakin duniya baki daya.

Quduri Babban qudurin wannan Majalisa shi ne, samar da wata makoma ta ilimi irin na Shari’ar Musulunci, wanda zai zama sanadi kuma ginshiqin daukaka da cigaba da bunqasar al’ummar musulmi da suke cikin wannan yanki na Afrika.

Nauyi       Babban nauyin da yake kan wannan Majalisa shi ne rayawa, ingantawa tare da fitowa da qoqarce-qoqarcen malaman nahiyar Afrika, da haxa kansu a matsayin tsintsiya madaurinki daya, domin hakan ya ba su cikakkar damar jagorancin al’umominsu a bisa ingantaccen tafarki Addinin Musulunci.

Dalilan Massasa Majalisar[gyara sashe | gyara masomin]

     Akwai manyan dalilai, da suka haifar da tunanin kafa wannan majalisa, da suka haɗa da;

  1. Rashin wani zaure qwara daya, da ake da shi a wannan nahiya, a matsayin makoma da musulmin Afrika a cikin al’amurra na ilimi.
  2. Rashin sauti daya, da yake wakiltar gaba dayan Al’umman musulmin wannan nahiya, idan ana zancen manyan matsaloli, da suka shafe su a matsayin al’umma.
  3. Yawaitar matsaloli da tashe-tashen hankula, da sauran nau’ukan gwagwarmayoyin rayuwa, wadanda musulmi suke cikinsu tsundum.
  4. Warwatsewar qoqarce-qoqarcen malaman da’awa, da rashin hadin kan da yake tsakaninsu.
  5. Rashin isasshen ilimi da zai bayar da damar bayar da ingantattun fatawoyi.[2]

Manyan Dokokin Gudanarwa[gyara sashe | gyara masomin]

      Manyan dokokin gudanar da wannan Majalisa a matsayin siyasar tafiyarwa, sun hada da:

  • Aiki da Alqur’ani da Sunna bisa fahimtar magabatan farko shiryayyu, bisa aqida matsakaiciya, wadda babu zurfafawa ko kasawa a cikin ta.
  • Kula da gaba dayan yankunan wannan nahiya ta Afirka komai nisan su, ta bangaren kafawa da gudanarwa, tare da samar da wakilci na haqiqa daga kowane yanki na nahiyar.
  • Gudanar da ayyukan Majalisa bisa tsari na cikakken gashin kai, tare da nisantar karbar umarni daga kowace irin kasa ko kungiya.
  • Kulla kyakkyawan zumunci da gaba dayan al’umomin nahiyar Afirka, ta hanyar alkinta matsayin wakilansu, tare da shirya taruka a kasashe da garuruwansu, wadanda suke dauke da sako mai ma’ana da manufa da kamanni iri daya.
  • Amfani da kwararru a fagen ilimi da aiki, domin daukar matakai da yanke shawarwari, da bayyana fahimta da ra’ayoyi.
  • Dogara a kan hanyoyi da dabaru irin na hikima da fasaha a fagen ilimi, domin mu’amala da wasu qungiyoyi masu zaman kansu, da ma’aikatun Gwamnati, da sauran vangaroran al’umma, wadanda ba fahimtarmu daya ba, da su.
  • Yin cikakken amfani da hanyoyin sadarwa da kafofinta, na zamani a fagen yadawa da isar da saqonnin Majalisar a fadin nahiyar ta Afrika.
  • Majalisar kuma, za ta bude kofofinta ga maza da mata, da suke son yin aiki tare da ita, amma, bisa sharudda da qa’idoji irin na Shari’ah.

Gurace-gurace[gyara sashe | gyara masomin]

Gurace-guracen wannan Majalisa sun hada da:

  • Samar da wata makoma ta ilimi da da’awa, wadda za ta riga daidaitawa da kuma tsara yadda ya kamata qoqarce-qoqarcen malamai, na ilimi da da’awa, su gudana a wannan nahiya ta Afrika.
  • Samar da qasaitacciyar makoma ta Musulunci, wadda za ta riqa magana da yawun musulmin nahiyar Afrika, a duk lokacin da aka hadu da qungiyoyi da ma’aikatu na ilimi da jami’an gwamnatocin qasashe da kuma na qasa da qasa.
  • Bayar da gudunmawa tare da raya qoqarce-qoqarcen da malamai suke yi na karantarwa da ilmantarwa ga al’umomin wannan nahiya ta Afrika.
  • Karfe kakakin fatawa daga hannun wadanda ba su cancanta ba, musamman a cikin manyan al’amurra da suka shafi gaba daya al’ummar nahiyar Afrika.
  • Samarwa tare da inganta zaman lafiya tsakanin manya da qananan al’umomin nahiyar Afrika.
  • Samarwa tare da bude kafafen sadarwa domin hulda da wasu Majalisu da qungiyoyi na Musulunci masu irin wannan hidima da kula da al’amurran al’ummar musulmi.  

'Hanyoyi Domin tabbatar da cin nasarar gudanar da wasu gurace-gurace, wannan Majalisa za ta bi hanyoyi kamar haka:

  1. Shirya yadda al’amurran ilimi da da’awa da tarbiyya za su riqa gudana a wannan nahiya ta Afrika.
  2. Kafa wuraren gudanar da hidimomi irin na ilimi da da’awa da tarbiyya, da kuma kula da su.
  3. Bunqasawa da qarfafa qungiyoyi da cibiyoyin harkokin Musulunci na cikin gida da qananan yankuna.
  4. Bugawa tare da watsa bayanai a kan manyan al’amurran da suka shafi al’umma, ta hanyar kafafen sadarwa.
  5. Gabatar da nasihohi da gargadi da luraswa ga dukan bangarorin da suke bukata.
  6. Yin tsaye tsayin daka a kan ganin an warware rikittan da suka shafi musulmin wannan nahiya.
  7. Bayar da fatawa a kan manyan al’amurra da sabbin matsaloli.
  8. Shirya taruka manya da qanana irin na ilimi da da’awa, tare da shirya taruka irin na qara wa juna ilimi da za su shafi gaba dayan nahiyar.
  9. Shirya wadansu taruka irin na koyarwa da habaka hikima da fasaha, don amfanin ‘ya’yan wannan nahiya masu baiwa ta musamman.
  10. Shiryawa tare da bugawa da yada ayyukan bincike da nazari.
  11. Samar da wadansu shiraruwa wadanda za a riqa saurare da kallo, a cikin harshen Gwamnatocin qasashe da qabilun Afrika.
  12. Samarwa tare da amfani da gaba dayan kafofin sadarwa
  13. Raya Masallatai da mimbarorinsu, da kuma samar musu da limamai da malamai wadanda suka cancanta, domin saqon da suke isarwa ga al’umma ya zama nagartacce.
  14. Samar da tsararrun bayanai da suke magana a kan Musulunci, a wannan nahiya ta Afrika, wadanda za su bayar da cikakkar damar nazarin Musulunci da sanin makamarsa a sauqaqewa.[3]

Qa’idojin Zaɓen Mambobi[gyara sashe | gyara masomin]

Qa’ida ne kafin a zabi mutum a matsayin manba a wannan Majalisi, ya cika wadannan sifofi:

  • Lallai ne ya kasance mutum mai cikakken tasiri da fada a ji a yankinsa.
  • Lalle ne ya kasance mai kyakkyawan tarihi; ba wanda ya shahara da ayyukan barna da badala ba.

Tsare-tsaren Bunqasa Ayyukan Mambobi[gyara sashe | gyara masomin]

Saboda bukatar da take akwai ta bunqasuwa tare da inganta ayyukan mambobin wannan Majalisa a tsakanin jama’arsu, wannan Majalisa ta dauri aniyar gudanar da wadansu tsare-tsare, da gabatar da wadansu hidimomi zuwa gare su. Amma, da sharadin rashin kasancewar wadannan abubuwa samammu gare su qarqashin tanade-tanaden da suke hannun cibiyoyi da sauran qungiyoyin abokan aiki, da suke kula da irin wannan hidima ta da’awa da sauran ayyukan Musulunci, a yankunasu. Wadannan tsare-tsare sun haɗa da:

  1. Samar da adiresai da sauran shafukan ilimi a yanar gizo, da za su sauqaqe hanyar watsawa da yada karance-karance da fatawowinsu.
  2. Alkinta yanayin Masallatai, da gina cibiyoyi, da samar da dakunan karatu.
  3. Tabbatar da ganin an nada an kuma watsa aikace-aikacensu na ilimi da da’awa, tare da kusantar da su ga al’umma da sauran daliban ilimi.
  4. Shirya taruka irin na bayar da horo domin bunqasa yanayin  jagoranci da tasiri da qwarewar da suke da shi.

Tsarin Shugabanci[gyara sashe | gyara masomin]

Manyan Ginshiqai

  • Al-Jam’iyyatul Ámmah (Mahadar dukan mambobi)
  • Al-Mu’utamarul Ám (Taron wakilai na ko ina)
  • Al-Majalisul Ám (Babbar mahadar shugabanni)

Majalisar Zartaswa:

  • Arri’ásah (Shugabancin Majalisa)
  • Al’amanatul Ámmah (Sakatariya)
  • Al-Lijánul Fanniyyah wal- Far’iyyah Addá’imah (Kwamitoci na ayyuka na musamman da kuma na din-din-din)

Qa’idojin Zaben Babban Ofishi Kafin a zabi wuri a matsayin inda za a kafa babban ofishin wannan majalisa, sai an yi la’akari da wadannan abubuwa kamar haka: o  Rinjayen Musulunci a wurin. o  Rinjayen Sunnah a wurin. o  Rashin tashe-tashen hankali irin na Siyasa. o  Sassafcin dokokin rajista da ayyukan qungiyoyi. o  Qaqqarfan asasi irin na a zo a gani a fagen na’urorin sadarwa. o  Wadatar rukunnai da muqarraban gudanar da ayyukan Musulunci.[4]

Matakan Kafa Majalisar Mataki na Farko: Tunani Tunanin samar da qasaitacciyar makoma ta Musulunci a farfajiyar nahiyar Afrika, tunani ne da ya samu gindin zama a zukatan malamai da sauran masu ruwa da tsaki a cikin ayyukan Musulunci a cikinta. Sauran abin da ya rage kuma na wannan tunani, ya cigaba da bunqasa ne ta hanyar tattaunawa a tsakanin wadannan rukunnai biyu, a duk inda suka haxu a wasu taruka, da kuma ta hanyar kafafen sadarwa na zamani a matakin daidaiku. A haka har aka cimma mataki da qoqarin aiwatarwa. Sai dai akwai bukatar samar da wani rukuni da zai kula da tuntuba da bibiya, da kuma tanade-tanade na wajibi.

Mataki na Biyu: Kafawa Bayan gudanar da shawarwari da musayar tunani da nazari, sai aka cimma matsayin cirata daga wannan mataki zuwa mataki na gaba, wato kafawa. Wadanda kuma aka tuntuba a lokacin gudanar da wadannan shawarwari sun hada da:

  1. Dr. Muhammad Ahmad Lauhu, daga Senegal
  2. Dr. Sa’id Muhammad Baba Sílah, daga Málí
  3. Dr. Muhammad Sani Umar, daga Najeriya

Bayan haka ne fa, aka samu kammala samar da asasin wannan Majalisa a cikin qwaqwalwa, a kan hanyar ciratar da shi zuwa haqiqa. Wadannan bayanai ma da muke gabatarwa yanzu suna daga cikin wadancan tsare-tsare.

Mataki na Uku: Bayar da Sanarwa Wannan shi ne babban mataki kuma ginshiqi a fagen qoqarin kafa wannan Majalisa. A wancan mataki na kafawa, mambobinsa sun riga sun samar da asasi na farko, wanda a cikinsa aka amince da zabar wadansu zaqaquran malamai na wannan nahiya ta Afrika, wadanda za su zama su ne mambobin kwamitin tabbatarwa da kafa Majalisar, da suka hada da:

§ Dr. Muhammad Ahmad Lauhu, daga Senegal § Dr. Sa’id Muhammad Baba Sílah, daga Málí § Dr. Muhammad Sani Umar, daga Najeriya §  Dr. Bashir Adam, daga Ghana §  Dr. Sa’id Burhan, daga Juzrul- qamar §  Dr. Musa Fadiga, daga Sahilul- Áj §  Dr. Yahaya Abdallah Ahmad, daga  Chadi §  Shaikh Khalfan Khumais, daga Kenya §  Shaikh Gahutu Abdalkarim, daga Ruwanda §  Shaikh Muhammad Zainu Zahruddin, daga Ethopia §  Shaikh Salim Bar Hayyan, daga Tanzaniya §  Shaikh Bilal Isma’il, daga Afrika ta kudu

Ba tare da wani bata lokaci ba, sai wannan kwamiti ya shiga aikinsa gadan-gadan, ta hanyar amfani da kafafen sadarwa na yanar gizo da sauran shafukan sadarwa na zamani, da tattaunawa ta hanyar waya. A karshe, aka yanke shawarar haduwa a birnin Makkah mai alfarma, a daidai lokacin gudanar da aikin Umra, domin gudanar da tattaunawa ta qarshe a kan yadda wannan Majalisa za ta kasance, da kuma bayar da sanarwa a kan ta, daga wannan bigire, inda hasken Musulunci ya samo asali. Wannan haduwa kuwa ta kasance ne tsakanin 7-12 ga watan rabi’us sání 1432H wanda ya yi daidai da 9-14 ga watan Maris 2011, wanda takwas daga cikin mambobin wannan kwamiti suka samu halarta. A qarshen wannan haduwa kuma an yi matsaya a kan wadannan abubuwa:

1)   Tabbatarwa tare da shimfida tsarin asasin wannan Majalisa.

2)   Shirya tsare-tsaren gudanar da babban taron qaddamarwa, da ambata inda za a yi. A qarshe, aka amince da gabatar da taron a Bamako babban birnin qasar Mali, a tsakanin 7 zuwa 9 ga watan Rajab 1432, wanda ya yi daidai da 8 zuwa 10 ga watan 7 na 2011. Daga baya kuma aka aminta da daga shi zuwa 9 zuwa 11 ga SSha’aban 1432, wanda ya yi daidai da 8 zuwa 10 ga Yuli 2011.

3)   Zabe tare da samar da jerin sunayen wadanda za su zama mambobin farko, zakarun gwajin dafi, gwargwadon masaniyar da su ‘ya’yan wannan kwamiti suke da ita a kan kowane daya daga cikinsu. Sa’annan kuma a bar kofar zauren a bude domin bayar da damar cigaba da zaqulo irin wadannan mutane, da suka cika sharuddan da aka gindaya tun da farko. Babbar matsalar da aka fuskanta a wannan mataki, ita ce samun cikakken adireshin mutanen da aka ga dacewarsu, balle a iya sanar da su. Sai dai kawai aka sha alwashi tare da lasar takobin tabbatar da ganin an isar musu da wannan saqo ta kowane hali, bayan wannan taro, domin su samu damar halartar taro na gaba wanda shi ne mafi muhimmanci, sai kuwa wanda samun adireshin nasa ya faskara.

4)   Samar da wata cibiya, wadda za ta yi riqon qwarya na jagorancin wannan Majalisa, wadda kuma ita ce za ta tsara yadda wannan babban taro na qaddamarwa zai kasance.

5)   Zana taswirar tsare-tsaren da suka zama dole don shiryawa da gudanar da wannan taro na qaddamarwa.

6)   Samar da jadawalin tabbatar da gurin wannan Majalisa na shekaru hamsin nan gaba.

7)   Tuntubar manyan qungiyoyin bayar da agajin ayyukan alhairi, na Afrika domin nemo gudunmawar gudanar da wannan taro.

Babban Taro[gyara sashe | gyara masomin]

Allah, cikin ikonsa an samu gudanar da wannan babban taro na qaddamar da wannan Majalisa kamar yadda aka tsara; a garin  Bamako, babban birnin qasar Mali, wanda baqi da daman gaske daga wannan nahiya ta Afrika da wajenta suka halarta. Daga wannan lokaci ne kuma aka bayar da sanarwar kafuwar wannan Majalisa ta Malaman Afrika. Lokaci wanda, daga bayansa ne kuma aka shiga aiki gadan-gadan, a matakin ginawa, da aiki irin na hadin guiwa.

Abokan Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Tun lokacin da wannan Majalisa ta karbi zanannen sunanta, take neman abokan aiki irin ta, wadanda suka damu da al’amurran Musulunci a fadin wannan nahiya ta Afrika, domin ta hada hannu da su. Ta kuma yi haka ne sakamakon nazarin qwaqwaf tare da shata bangaroran da ake da bukata da wannan qawance a cikin su. Wannan qawance kuma, abu ne mai sauqi, ya wuce iyakokin wannan nahiya ta Afrika, ya hada har da wadansu bangarora na musayar dabaru, da sha’anin kudi, da kwarewa, da tsare-tsare a wasu bangarora da al’amurra daban-daban.

Kammalawa[gyara sashe | gyara masomin]

Mafi girman abin da ya kamata mu kalla a daidai wannan mataki, shi ne abin da Allah Madaukakin Sarki ya gaya wa Annabin sa sallallahu alaihi wa sallam, wanda shi ne jagora, kuma babbar Makarantarmu, wato: “Kuma ka yi shawara da su a cikin al’amari. Kuma idan ka yi azama, to, ka dogara ga Allah. Lalle ne Allah yana son masu tawakkali.”  Suratu Ali Imran: 159 Alhamdu lillah[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Ofungiyar Schowararrun Malaman Afirka, membobin ofishi, an adana kwafin Yuni 23, shekarar 2017, a kan Injin Wayback
  2. Ganawa da karatun Afirka Babban sakatare [gurguntaccen haɗin yanar gizo] Kwafin da aka ajiye 05 Maris 2016 akan Na'urar Wayback
  3. Babban sakatare na Portal Islamic Kwafin da aka kebe ranar 21 ga Satumba, 2015 a kan Wayback Way
  4. A kan batun Rohingya Sakatare-Janar Babban kwafi An adana Janairu 1, 2016 a kan Wayback Way
  5. Kofar Musulunci, kwafin da aka ajiye ranar 21 ga Satumba, 2015 a kan Wayback Way