Malaysian Indian cuisine
Abinci na Indiyawan Malaysia, ko abinci na al'ummomin Indiyawan dake Malaysia, ya ƙunshi daidaitawa da ainihin jita-jita daga Indiya, da kuma abubuwan da'aka kirkira na asali da al'adun abinci daban-daban na Malaysia sukayi wahayi zuwa garesu. Saboda yawancin al'ummar Indiyawan Malaysia sun fitone daga asalin Kudancin Indiya, kuma galibi 'yan kabilar Tamils ne waɗanda suka fitone daga yankin tarihi wanda ya ƙunshi jihar Indiya ta zamani ta Tamil Nadu da Lardin Arewacin Sri Lanka, yawancin abincin Indiyawan Malaysia galibi sun samo asali ne daga Kudancin India a cikin hali da dandano. Wataƙila za a dafa abinci na Indiya na Malaysia tare da ganyen curry da kayan yaji guda ɗaya, kuma ya ƙunshi sabon kwakwa acikin siffofi daban-daban. Har yanzu ana amfani da Ghee sosai don dafa abinci, kodayake mai na kayan lambu da mai na dabino yanzu sun zama ruwan dare acikin gidajen abinci. Kafin cin abinci al'ada ce a wanke hannaye kamar yadda ba'a amfani da kayan abinci yayin cin abinci, banda cokali don kowane abincin.