Jump to content

Man Alayyadi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Gabatarwa[gyara sashe | gyara masomin]

Al'ummar kasar Maroko sun kasance su na amfani da Man alayyadi shekaru aru-aru da suka gabata - ba wai kawai saboda maikonsa, ko kara dandanon abinci ba, sai dai saboda fa'idodin kiwon lafiya da yawa da Man alayyadi ke dauke da su.[1]

Ana samun man alayyadi daga 'ya'yan bishiyar "Argan" a turance, kuma su 'ya'yan wanan bishiya sun yi kama da 'ya'yan kwakwar man ja da muke da ita a kudancin wannan kasa ta mu. Hakanan, ana kira man alayyadi da "Argan Oil" da turanci.[2]

Ko da yake asalin bishiyar "Argan" ko kuma shi man alayyadi ƙasar Maroko ne, amma a yanzu ana amfani da man alayyadi a duk faɗin duniya don dafa abinci iri-iri, kayan kwalliya da kuma magani.

Saboda matukar muhimmmanci da man alayyadi ke da shi ga lafiyar al'umma, Mujalla ta yi dogon nazari da bincike, inda daga karshe mu ka gano amfanin man alayyadi guda goma sha daya (11) ga lafiyar Dan- adam.

Amfanin Man Alayyadi[gyara sashe | gyara masomin]

Man Alayyadi Ya Kunshi Mahimman Sanadirai Masu Gina Jiki Da farko Man alayyadi ya ƙunshi fatty acids da kuma sanadarin phenolic mai yawa, wadanda sanadarai dake kan gaba wajen samar wa jiki koshin lafiya . Kusan 29-36% na sanadaran fatty acid dake kunshe cikin man alayyadi ya samuwa ne daga linoleic acid, ko omega-6, inda ya ke juya shi zuwa kyakyawan mai dake samar da nau'ikan sandarai ma su gina jiki. Oleic acid, ko da yake ba shi da mahimmanci, yana da Kashi 43-49% na fatty acid, amma irin wannan sanadari dake ciki man alayyadi kuma yana da lafiya sosai. Ana iya samun wannan snadari a cikin man zaitun kuma, oleic acid ya shahara saboda ingantaccen tasirin sa akan lafiyar zuciya. Bugu da ƙari, masana na sanya man alayyadi a cikin jerin mayukan da ake ganin sune tushen bitamin E, wanda ake buƙata don lafiyar fata, gashi da idanu. Wannan bitamin[3] kuma yana tattare da sandaran antioxidant masu yawan gaske.

1.Man Alayyadi ya Na Kara Lafiyar Zuciya[gyara sashe | gyara masomin]

Man Alayyadi shine tushen sanadaran oleic acid, wanda shine kitse mai kunshe da omega-9 fatty acid. Hakanan ana samun Oleic acid a cikin man alayyadi baya ga samun irin wannan sanadari a wasu nau'ikan abinci da yawa, kamar avocado da man zaitun, kuma galibi ana danganta shi wannan sanadari da tasirin wajen bai wa zuciya kariyar daga kamuwa daga cututtuka . Ɗaya daga cikin wani binciken da aka gudanar ya lura cewa man alayyadi yana kama da man zaitun a cikin ƙarfinsa don rage haɗarin cututtukan zuciya ta hanyar bunkasa sanadaran antioxidant a cikin jini. A cikin wani binciken da aka gudanar dabam, ya nuna cewa, yawanta amfani da man alayyadi yana da alaƙa wajen rage kitsen da ake kira "cholesterol" da turanci wanda an sami yana haifar da matsala a jikin dan adam, a gefe guda kuma, yawan shan man alayyadi na kara yawa sanadaran "antioxidants" wadanda ke bai wa jiki kariya daga cututtuka.[4] A wani bincike kuma da aka gudanar dangane da haɗarin kamuwa daga cututtukan zuciya a cikin mutane 40 masu lafiya, waɗanda suka yi amfani da giram 15 na man alayyadi kowace rana tsawon kwanaki 30 sun sami raguwar kashi 16% da 20% a cikin 100 na kitsen kwalastaral.

Man Alayyadi Na Bada Kariyar Kamuwa Da Ciwon Suga[gyara sashe | gyara masomin]

Wasu binciken baya-bayan nan da masana suka gudanar ya nuna cewa, amfani da man alayyadi na iya taimakawa wajen hana kamuwa da ciwon suga. Nazarin da aka gudanar ya haifar da raguwar sugan cikin jini da kaso mai yawan gaske. An gwada wannan bincike ne, kan wasu berayen inda ake ciyar da su abinci mai kunshe da suga mai yawan, sannan kuma ake ba su man alayyadi don a gano tasirinsa wajen hana kitsen cikin jini wanda ke haifar da ciwon suga. Ko dayake, a gefe guda, wasu masanan suna da ra'ayin cewa, irin wannan sakamakon ba lallai ba ne ya nuna cewa za a ga irin wannan tasiri a jikin mutane. Don haka, ana buƙatar gudanar da irin wannan binciken a jikin ɗan adam.

Man Alayyadi Na Bada Kariyar Kamuwa Da Ciwon Daji[gyara sashe | gyara masomin]

Man Alayyadi na iya jinkirta ko hana girma wasu nau'ika na ƙwayoyin cutar ciwon daji wato "Cancer". Ɗaya daga cikin binciken da masana su ka gudanar, sun yi amfani da sanadaran polyphenolic da aka samar daga man alayyadi akan kwayoyin cutar daji da ake kira "prostate cancer" a turanci. Sakamakon da aka samu ya hana girman kwayar cutar daji da kashi 50% cikin 100. Hakanan, a wani binciken, an cakuda man alayyadi da bitamin E, sakamakon da aka sanu ya nuna yawan mutuwar kwayar cutar kansa ta nono da ta hanji. Kodayake, a gefe guda wasu masanan na ganin cewa, duk da yake wannan bincike na farko ya bayar da sakamako mai ban sha'awa, amma ana buƙatar ƙarin bincike don sanin ko za a iya amfani da man alayyadi don magance ciwon daji kwata-kwata.

Man Alayyadi Na Kara Inganta Lafiyar Fata[gyara sashe | gyara masomin]

Man alayyadi ya shahara kwarai da gaske wajen inganta lafiyar fata, inda ya ke rage alamun tsufa ga fata. Wasu bincike sun nuna cewa cin abinci na man alayyadi na iya taimakawa wajen rage tsufan fata ta hanyar rage yankwanewar fatar. Hakanan yana iya tallafawa wajen gyarawa da samarwa da lafiyayyer fata idan aka shafa man alayyadin kai tsaye a jikin fata. Wani nazarin ya nuna cewa, anfani da man alayyadi ta hanyoyi biyun da aka ambata a sama, wato ko dai ayi amfani da shi a cikin abinci ko kuma a shafa shi kai tsaye a jikin fata, hakan na yin tasiri don haɓaka laushi da shekin fata .[5]

Man Alayyadi Na Iya Magance Wasu Cututtukan Fata[gyara sashe | gyara masomin]

Man Alayyadi ya kasance sanannen maganin da ake amfani da shi a gida ko ta hanyar gargajiya don magance wasu cututtukan fata kamar kumburi, shekaru da yawa da su ka gabata ,musamman a kasashen dake yankin Arewacin nahiyar Afirka, inda daga nan ne bishiyoyin "argan" da ake samun man alayyadi ta samo asali. Kodayake akwai takaitattun nazarce-nazarcen kimiyya na zamani a kan hakan, amma dai an yi amfani da man alayyadi ta hanyar gargajiya kan wasu cututtukan fata, kuma an ga tasirin hakan. Duk da haka, wasun binciken da aka gudanar a wannan zamanin ya nuna cewa man aalayadi ya ƙunshi nau'o'in sanadaran "antioxidant" da "anti-inflammatory", wandanda za su iya zama dalilan da za a iya amincewa kan ingancin man alayyadi game da matsalolin fata.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-31. Retrieved 2023-03-31.
  2. https://tozalionline.com/man-alaydi-da-anfanin-sa/
  3. https://mymemory.translated.net/en/Hausa/English/man-alayyadi
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-31. Retrieved 2023-03-31.
  5. https://hausadictionary.com/alayyadi