Jump to content

Mary Donington

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Mary Winifred Sylvia Donington, (shekara ta dubu data da Dari Tara da Tara zuwa shekara ta dubu data da Dari Tara da tamanin da bakwai) , mawaƙiya ce kuma mai zane-zane ta Burtaniya.

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Donington a Landan, ta yi karatu a Makarantar Mary Datchelor da ke Camberwell kuma tana da ilimin kiɗa na gargajiya a Royal Academy of Music . Kodayake ta kwashe shekara guda, daga shekara ta dubu daya da Dari Tara da arba'in da biyar zuwa shekara ta dubu daya da Dari Tara da arbar'in da shidda a matsayin ɗalibar mai zane-zane Frank Dobson ta kasance mai zane-zanen kai.

A lokacin da take aiki a matsayin mai zane-zane Donington ta kirkiro siffofin hoto a cikin tagulla, terracotta da gyare-gyare kuma ta nuna a Royal Academy, tare da Kungiyar Fasaha ta Mata ta Duniya, Society of Women Artists da National Society of Painters, Sculptors and Gravers / Printmakers . A shekara ta dubu daya da Dari Tara da arba'in da takwas ta nuna wani bus na Rosemary Cowper a Royal Glasgow Institute of the Fine Arts . [1]

Donington ya zauna shekaru da yawa a Headley Down a Hampshire kuma ana zaton ya mutu a can a watan Fabrairun shekara ta dubu daya da Dari Tara da tamanin da bakwai.

Bayanan da aka ambata

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. University of Glasgow History of Art / HATII (2011). "Mary Donington". Mapping the Practice and Profession of Sculpture in Britain & Ireland 1851–1951. Archived from the original on 27 September 2021. Retrieved 27 September 2021.