Jump to content

Maryam A baba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Marryam A Baba (sangadale) Fitacciyar mawakiya ce a masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud, ta Dade tana Waka tayi Wakoki da dama a masana'antar, tayi fice.[1]

Takaitaccen Tarihin ta[gyara sashe | gyara masomin]

[2]Maryam A Baba wato Maryam sangadale Haifaaffiyar jihar Kano ce , mawakiya a Masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud,an daura auren ta a ranar 24 ga watan ugusta shekarar 2019,inda ta auri mawaki Dan uwanta Mai suna Abdul kafinol Cikakken sunan sa Abdurrashid muhammad Ibrahim an daura auren ne a ranar asabar karfe Sha daya a kofar gidan su Dake unguwan sabuwar gandu a cikin birnin Kano, tayi wakar sangadale dalilin da ake mata lakabi dashi kenan,tayi Wakoki da dama.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://hausa.legit.ng/1254717-allah-ya-sanya-alkhairi-fitacciyar-mawakiya-maryam-sangandale-za-ta-amarce.html
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-26. Retrieved 2023-07-26.