Masa,uda Ibrahim

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Masa'uda Ibrahim Yar Agadaz jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud, sannan Kuma furodusa ce masana'antar fim tayi fina finai da dama a masana'antar yanzun take tashen ta. Ta fito a Shirin fim Mai dogon zango na Tashar Arewa 24 Mai suna DADIN KOWA inda ta fito a suna zuby , [1]shine fim din da ya daukaka ta a idon duniya kowa ya San ta.[2]

Takaitaccen Tarihin Ta[gyara sashe | gyara masomin]

Masa'uda Ibrahim an haife ta a ranar 13 ga watan [3]nuwamba a garin agadaz. Haifaffiyar kasar nijar ce ta girma acan tayi karatun firamare da sakandiri a garin agadaz. Bayan ta gama ta zo jihar Kano ta shiga masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud, an Fi sanin ta da yar agadez a masana'antar. Fim din da ya Kara fito da ita shine fim din"yar agadez " Wanda darakta aminu Saira ya Bada umarni , Umar S k mazugal yayi furodusin da Kuma nura Umar UK Wanda su kayi a shekarar 2011, tare da jarumi sani danja, Ibrahim maishinku,da Kuma nafisa Abdullahi, Zainab indomie, shine fim dinta na biyu a masana'antar. Tana kwaikwayon salon Tsohuwar jaruma safiya Musa, wacce suka zo suka zama kawaye. Ta shigo masana'antar fim a shekarar 2010 ta hannun furodusa Umar S K mazugal. Itace C.E.O na kamfanin Yar Agadez investment .[4]

Fina finan ta[gyara sashe | gyara masomin]

[5]

  • Yar Mai ganye
  • Daga aure na
  • Yar agadez
  • gidan mijinah
  • Wata mata ce
  • Gida uku
  • Rayuwa sirri ce
  • Ishara
  • inda Rai
  • Sama da Fadi
  • mugun zama
  • Mijin Fatima
  • mai laya
  • Daga aure na
  • Madafar kaunah

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://m.youtube.com/channel/UCT6mpU6GVo38dylNmIC8-1A
  2. https://www.hausaloaded.com/2019/11/hrkar-fim-na-kunshe-da-mahassada-cikin.html
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-31. Retrieved 2023-07-31.
  4. https://dimokuradiyya.com.ng/na-hadu-da-matsaloli-sosai-a-harkar-fim-cewar-masauda-yar-agadaz/
  5. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-31. Retrieved 2023-07-31.