Arewa 24

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Wikidata.svgArewa 24

AREWA24 tashar talabijin ce ta tauraron dan adam ta Najeriya wacce ake samu a DSTV, GOtv, da Startimes wanda ke nuna salon rayuwar Yankin Arewacin Najeriya . Tashar ita ce ta farko ta amfani da harshen hausa .

Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]

AREWA24 mallakar Equal Access ce kuma tana daukar nauyin shirye-shiryen al'adu da ilimantarwa ga mutanen arewacin Najeriya a cikin harshen hausa. Cibiyar sadarwar tashar ita ce Nilesat .

An kirkiro AREWA24 ne a shekara ta 2013 domin cike gurbi a cikin shirye shiryen nishadi da kuma salon rayuwa na harshen hausa. Kaddamarwar ta ci kusan dala miliyan bakwai kuma Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ce ta dauki nauyinta. Tashar ita ce tashar talabijin ta farko da ake gabatar da shirye-shiryenta 24/7 da harshen Hausa wacce ta samo asali daga gina zaman lafiya da nishadi . A cewar shafin yanar gizon Equal Access International, tashar na nufin fadada al'adun Arewacin Najeriya, tare da samar da alfahari da al'adu.

A shekara ta 2017, AREWA24 ta yi aiki tare da Eutelsat Communication don bunkasa damarta a matsayin tashar talabijin ta kyauta a yankin Kudu da Saharar Afirka don masu jin Hausa . A shekara ta 2018, tashar ta kara waka da wasanni a cikin harshen hausa. A wannan shekarar, AREWA24 ta kulla sabuwar kawance da kungiyar Girl Effect don tallafawa nasarar 'yan mata a arewacin Najeriya. Tashar ta kuma hada hannu da finafinan Kannywood da ke Kano, Najeriya .

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]