Jump to content

Matakan Aiwatar da Sassaka a Kasar Hausa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kowace sana'a ta tanadi was hanyoyi na musamman da mai gudanar da ita zai bi wajen gain ya samu aiwatar da sana'ar cikin nasara. Ga masu aiwatar da sana'ar sassaka musamman a Bahaushiyar al'ada, sun tanadi was matakai da masassaki zai bi domin ganin ya samar da wani abin sassaka. Duk da yake kayan bukatu sun bambanta daga wannan rukunin al' umma zuwa waccan, amma dai kusan duk zubi da tsarin sassakar iri daya ce. Don haka, domin samar da misali kawai, binciken ya dauki sassakan turmi, domin bayyana matakan da masassaka kan bi kafin samar da shi ga al' ummar Hausawa.

A kasar Hausa, turmi yana daya daga cikin muhimman kayan da masassaka kan samar, wanda mafi yawan al'umma ke amfani da shi a gidajensu ta fuskoki daban-daban. Wanna bincike ya gano kusan a ce da wuya a samu gidan Bahaushe da ba a amfani da turmi ko yaya yake duk da irin wayewar kai da ya shigo mu a wannan zamani. Haka saboda muhimmancin turmi da wuya ka ga an kai amaryar Bahaushe dakinta ba tare da shi ba. Duba daga irin wannan muhimmancin da ke damfare ga turmi, ya sa na zabe shi domin bayyana yadda ake aiwatar da sassakarsa a kasar Hausa. Duk da yake wannan misali ne kawai, amma kusan duk tsari daya ne da sauran sassake-sassaken da ake aiwatarwa a sassan kasar Hausa. Abin da ya bambanta sauran sassakan kawai shi ne irin nau' in abubuwan da ake so a sassaka. kafin a sassaka turmi akwai matakai daban-daban da mai aikin sassaka zai bi wajen aiwatar dashi, daga cikin wadannan matakai kuwa sun hada da:

  1. Zaben ice
  2. Kaya
  3. Katsa
  4. Kwakkwafa
  5. Fitarwa
  6. Kashe-daba
  7. Fid da siffa
  8. Shaba da kaifafawa
  9. Fitar da baki
  10. Tsayar da fasali

Ga dai yadda bayanan matakan daki-daki. Da farko mai

aikin sassakan turmi vana bukatar va tanadi

kayayyakin aiwatar da sassaka da suka hada da:

Gatari, gizago, masurhi (wambali), masarnayi (guru),

mahuri da dan tafe.

Bayan masassaki ya tanadi wadannan kayan

aiki ne zai tafi daji neman itacen da yake so ya yi

amfani da shi. Musa Sakke ya bayyana wasu daga cikin

itatuwan da suke amfani su sun hada da itacen kade ko

dalbejiya ko Kirya ko gawo ko madacci ko taura da

sauransu. Har wa yau, ya bayyana cewa, akwai a kalla

matakai goma da mai sassakan turmi zai bi kafin ya

samar da shi a cikin al'umma a Bahaushiyar al'ada.

1 Zaben Itace

Zaben itace shi ne mataki na farko da kowane

masassaki ya kamata ya fara kula da shi a kokarinsa na

samar da kowane irin abin amfani na sassaka. Don

haka, masu sassakan turmi sun ba wannan bagiren

muhimmanci domin samar da nagartaccen turmi a cikin

al'umma. Ana zaben itatuwan ne domin ingancin su ta

yadda za a dauki dogon lokaci ana amfani da su ba tare

da wata illa ba. Don haka, zaben itacen sassaka ga

masassaka shi ne mataki na farko da masassaki zai yi

la'akari da shi a wajen sassakan turmi.

2 kaya

Kaye shi ne mataki na biyu da mai sana'ar

sassakan zai yi a lokacin da yake Kokarin fara aiwatar

da sassakarsa. Kave shi ne saran itacen da ake bukatar

sassakar ya fadi Kasa. A wannan matakin, wani lokaci

masassaka na cin karo da wasu itatuwa masu iskoki da

saransu kan yi wuya, wani lokaci sai masassaki ya nuna

irin ta shi waibuwa ta yin wasu 'yan tsatsube-tsatsube

kafin ya iya kayar da itacen kasa.

3 Katsa

Bayan an kayar da itacen a kasa, mataki na

uku da mai sassakan zai yi shi ne katsan itacen da ya

kayar. Katsa a nan na nufin sare itacen da aka kayar

zuwa gunduwa-gunduwa dai-dai vadda masassaki ke

bukata. A wannan matakin masassaki kan fid da nau'in

gunduwar itacen da yake bukata wurin fid da irin siffar

ko girman da turmin da yake so ya sassaka. Misali

babba ne ko karami, idan babba yake bukata tilas a samu babbar gundurwar itacen. Idan kuwa karami ne, sai a samu gundurwa Karama.

4 Kwakkwafa

Bayan masassaki turmi ya yi katsa, abu na gaba shi ne mataki na hudu wato kwakkwafa. Ita dai kwakkwafa wata dabara ce ta kwakkwafar gunduwar itacen da aka katsa ta hanyar cire bawon da ke jikin gunduwar, da daidaita jikin katsar ta yadda za a ji dadin aiki da shi. Wani lokaci a wannan mataki ne masassaka suke auna tsawo ko gajartar turmin da suke son sassakawa ta amfani da igiya ko kamun hannu ko Kafa.

5 Fitarwa

Kamar yadda sunan ya nuna, a wannan matakin ne na biyar inda ake ginan turmin zuwa yadda ake bukata. A nan za ga cewa, zurfin turmi ya danganta ne gwargwadon irin amfanin da za a yi da shi bayan an kammala shi. Galibi ana amfani da masuri ne ko wambali wajen ginan turmi a kasar Hausa. Shi kuwa masurhi haka yake kamar fartanya, amma Kotarsa ta fi ta fartanya tsawo, kuma bakinta ya fi na fartanya kauri da tsayo. Wannan siffar ma'aikacin it ke ba masassaki damar ginan gunduwar itatuwan da ya kata kamar yadda yake so.

A Wannan matakin ana aiwatar da shurin

turmi a lokacin da aka gama ginan turmi da masurhi ko wambali. Shurin turmi kamar ginar turmi yake, sai dai shi ana amfani da guru ne wajen Kara wa turmi zurfi.

Guru wani ma'aikaci ne da masassaka ke amfani da shi domin Kara zurfin abin da suke sassaka musamman idan abin da ake sassaka zurfinsa matsastse ne, don haka shi wannan ma'aikacin (guru) bai kai masurhi girma ba. kuma akwai babba akwai karami.

6 Kashe Daba

A lokacin da masassaki ke aiwatar da sassakar

turmi, can a tsakiyar turmin za a samu wata mahada da masassaki ke tsayar da sassakarsa a tsakiyar turmi. A wannan mahada ce masassaki ke tsayar da sassakar da ya faro tun daga saman turmi daga ciki har zuwa wannan dabar. A na kiransa kashe daba ne gain duk sassakar da aka yo musamman na cikin turmi a nan ne ake tsayawa. Shi wanna kashe dabar yana da alamar tuntu da wanzamai a Kasar Hausa kan vi a kan vara wajen aski a shekarun baya. Ita kuwa wannan dabar, galibi ana sassake ta ne bayan an gama shata yadda ake so turmin ya kasance, watau fadinsa da zurfinsa.

7 Fid Da Siffa

A nan za a fid da gindin turmi, gindin turmi wani bangare ne mai muhimmanci ga mai sassakar turmi. Gindin turmi yana nufin mazaunin turmi ta yadda za a iya ajiye shi ya tsayu ana amfani da shi. Kamar yadda saman turmi yake a zagaye, haka shi ma gindin turmi a zagaye yake, amma ba tare da rami a tsakiyarsa ba. Haka gindin turmi bai kai saman turmi fadi ba.

Haka a wannan mataki ne za a fid da kafa. A

wannan mataki na fitar da Rafa, masassaki na amfani da gizago. Kafar tana nufin marikin turmi inda ake sa hannu a dauke shi daga wannan wuri zuwa wancan.

8 Shaba Da Kaifafawa

A wannan mataki ake fid da kaifin Rafa. Shi

kaifin Rafa shi ne wani dan vanka da ake vi a kan Rafar turmi ta tsaye. Shi kuwa kashe kaifin Rafa ana vin sa ne ya doshi Kasan hannun turmi. Haka a nan ne ake shaba, shaba shi ne sassakan da ake yi a bayan turmi har sai turmin ya yi sumul ta yadda ba zai iva raunata wanda ya shafe shi ba ta hanyar yi masa tsartse. A wannan mataki na shaban turmi, ana yin sa ne da gatari Karami. Daga nan sai ya yi lailaya. Shi lailayar turmi tamkar shaban turmi ne, sai dai a yayin da ake amfani da gatari wurin shaban turmi, a wajen lailayar turmin kuwa ana amfani ne da gizago. Wannan lailayar da ake wa turmi shi ma yana Kara inganta siffar turmi ya zama gwanin ban sha'awa. Yin wannan kan Kara wa turamen gwarjini ga masaya. Don haka, lailaya ita ce sassakan bayan turmi da masassaki kan yi da gizago domin sassakar ta yi kyau ba tare da samun kware ko tudu a jikin turmin da ake sassaka ba.

9 Fitar Da Baki

Yankan bakin turmi na sama shi ne mataki na

gaba da mai aikin sassakan turmi zai aiwatar. A wannan muhallin na yankan bakin turmi, masassaki na amfani da gizago ne wajen daidaita bakin turmin da yake sassaka daga saman turmi. Yin wannan shi zai sa a samu daidaiton bakin ta yadda wani sashe nasa ba zai wuce wani sashe ba. Haka a wannan mataki bayan an kammala aikin sassakar turmi, masassaki zai yi amfani da gizago wajen kashe kaifin sassakarsa da ya yi na turmi ciki da waje. Wannan na faruwa ne bayan an yi yankan bakin turmi, gefensa na kasancewa da kaifi ta yadda zai iya yi wa wani rauni, don haka sai an kashe kaifin ta hanyar sassakar gefen bakin turmin

10 Tsayar da Fasali

Wannan mataki shi ne na Karshe, wannnan mataki shi ne gyaran da ake wa gindin turmi a Rasansa ta yadda zai samu girkuwa ya tsayu ana amfani da shi a lokacin da bukatar haka ta samu. Domin kuwa ba tare da yin wannan aikin ba, turmin ba zai samu tsayuwa a yi aikin da ake bukata da shi ba.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]