Jump to content

Mercedes-Benz Vision AVTR

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mercedes-Benz Vision AVTR
concept car (en) Fassara da battery electric vehicle (en) Fassara
Bayanai
Color (en) Fassara silver (en) Fassara
Manufacturer (en) Fassara Mercedes-Benz Group (en) Fassara
Brand (en) Fassara Mercedes-Benz

Mercedes-Benz Vision AVTR mota ce da aka kera a matsayin prototype wadda aka fara nunawa a taron Consumer Electronics Show, wato (CES) na shekara 2020. Motar ta samo tushe ne daga film din James Cameron wato "Avatar". Kalmar ta AVTR da yake jikin sunan motar na nufin Advanced Vehicle Transformation wanda ya samo asali ta dalilin hadin gwiwa tsakanin kamafani dauka da shirya fina-finai ta Amuruka wato Disney da kuma kamfanin kerawa da sarrafa motoci na germany wato Mercedes.

Ita dai wannan motar alama ce dake nuna yadda kamfanin motoci na Mercedes ke tunanin kasancewar goben tsari da kuma zanen motoci. Wannan mota dai har yanxu ba'a sake ta ba zuwa ga al'umma. An ajiyeta ne a matsayin prototype wacce zasu duba domin kera ire-irenta a nan gaba idan lokacin shigowarta kasuwa yayi.

Zane da Mahangar motar[gyara sashe | gyara masomin]

Zanen motar na kunshe da nauika daban daban na siffofi kamar su circle, triangle da dai sauran makamantansu. An tsara jikin motar na waje wato exterior ta hanyar amfani da layuka da kuma nauikan siffofi dake nuni da rayuwar gaba. Tsarin cikinta kuwa an yisa ta yadda zai alakanta direba da fasinjoji da kuma ita kanta motar.

Tsare Tsare.[gyara sashe | gyara masomin]

Kamar yadda Mercedes suka wallafa a yayin da suke gudanar da taron nuna wannan mota, sun fada cewa motar zata zo da abubuwa kamar haka:

  • Autonomous Drive wato tukin kai da kai wanda aka fi sani da driverless mode
  • Brain-Computer Interface wato BCI wanda zai bada damar motar tayi connecting din kanta da kwalwar dan adam domin samar da yanayin tuki mai gamsarwa ga direba da kuma fasinjoji.
  • Heartbeat-Synchronization: Zata zo da tsarin da zai bada damar direba ya bata ikon lura da bugun zuciyar sa tare da nuna yanayi wanda yayi kamanceceniya da yadda zuciyarsa ke harbawa.
  • Based Battery: Zata zo da tsarin battery ba man fetur ba. Maana zaa dinga caza ta ne idan tayi kasa.
  • Tafiyar Kowane Lungu: Motar na da ikon yin tafiya ta gefe-gefe ko gaba ko baya domin samar da yanayin tuki mai sauqi tare da gamsarwa ga shi direba. Hakan zai yiwu ne ta hanyar amfani da tayoyi dake masu kama da kwallon kafa.

Hotuna[gyara sashe | gyara masomin]

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

[1] [2]

  1. https://www.mercedes-benz.com/en/innovation/concept-cars/vision-avtr/
  2. http://www.youtube.com/watch?v=oO_KgtIuaEo