Muhammad Tukur Abdullahi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Muhammad Tukur Abdullahi wanda akafi sani da Mallam, (An haifeshi ranar 1 ga watan Mayu, 1936), ga iyalin Galadiman Katsina, karamar hukumar Malumfashi. Ya kasance likita, wanda ya rike matsayin Babban Chiyaman na cibiyar kula da lafiya wato (Health Management Board) na tsohuwar jihar Kaduna daga bisani kuma Babban chiyaman na (Family Support Trust Fund) a lokacin mulkin Gen. Sani Abacha.

Kuruciya da Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Mahaifinsa Alhaji Abubakar shine Galadiman Katsina daga karamar hukumar Malumfashi, mahaifiyarsa kuma Hauwa ta fito ne daga gidan sarauta itama. Ya fara karatun Qur’ani tun yana da shekaru 5, sannan ya fara karatunsa na firamare a katsina central elementary school dake Rafukka Quarters acikin tsohon ginin Kwalejin Katsina.

Ya kuma cigaba da karatunsa Middle School daga shekarar 1949 inda ya kammala a alif 1953, inda ya wuce makarantar ilimin magunguna ta Zaria (Pharmacy School) inda yanzu aka sani da ABU Zaria sannan ya zama likitan magunguna (Pharmacist) a 1957.

Ya samu tallafin gwamnati (Northern Nigeria Government scholarship) don fita kasar waje don cigaba da karatu a Uk.

Dr. Tukur ya sama kololuwar sakamako daga Norwood Technical College, London tsakanin 1961-1963 duk a UK. Ya dawo Jami’ar Lagos a don samun horon likitanci tsakanin 1963-1968. Ya samu sakamakon digiri na MB.BS a 1968 daga Jami’ar London. Ya koma UK don karatun digiri na biyu a Middlex University.

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Ya zama cikakken likita a asibitin Horarwa ta Zaria a tsakanin 1968-1970, sannan an turashi zuwa asibitoci daban daban. Har wayau kuma yayi aiki a asibitin Norwood Technical College London. Ya kuma rike mukamai a ma’aikatu da dama na gwamnati. Ya rike matsayin kwamishinan aiki na ma’aikatu kamar haka; Fannin Kudade (finance), Lafiya (Health), Kasuwanci (commerce) da kuma Masana’antu (industries).

An bashi matsayin Executive Chairman health management board, na tshouwar Jihar Kaduna, daga bisani kuma a ofishin shugaban kasa matsayin, Executive Chairman na Family Support Trust Fund a lokacin Abacha daga 1980 zuwa 1983 sannan kuma PTF.

Kungiyoyi[gyara sashe | gyara masomin]

  • Founding member of the west Africa college of Physicians
  • Former Vice president of Nigerian Association of physician
  • A member of the royal college of physicians
  • Member of board Nigerian and British medical associations
  • Fellow of Nigerian medical college of physicians

Muƙamai[gyara sashe | gyara masomin]

Ya rike shugaban (ciyaman) na wurare kamar haka:

  • EMI (Nigerian)
  • Jinya medical clinics limited
  • Arewa Astra pharmaceuticals limited
  • Health care security limited
  • Nigerian universal Bank ( as commissioner of commerce )
  • Trans Nigerian medical electronics and equipment company limited

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Ya auri mata biyu kuma dukkanninsu sunan su Bilkisu. Yana da ‘ya’ya 15 tare da su. Sannan kuma yana da jikoki da dama.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]