Nahwu
Abubuwan da yakamata kasani kafin kasan ilimin nahw
Kasani ilimin nahw yanada wasu ginshikai wadanda dasu ne dole zakasan ilimin nahw, kamar dai sauran ilimi. Wadannan ginshikai sune kamar haka;
1)ta'rifi (definition) 2)akan meye yake tattaunawa 3)me zaka amfana dashi idankakarantashi 4)meye alakarshi dasaura fanni ilimi(Darussa) 5)menene falalarshi 6)amfaninshi 7)sunanshi 8)ai'na aka samoshi 9)hukuncinshi 0)meya fi maida hankali akai
Wadannan sune ginshikanda aka gina ilimin nahw akai, dama dukkan ilimi gabadaya.
Yanzu zamu ɗaukesu ɗaya bayan ɗaya muyi bayani dalla-dalla akansu.
1)Idan amace ta'arifi (definition) ana nufin menene wannan abun Ma'anar Shi ayare (technically)ko a ilmance (definition), ko ya zakasan wannan abun. Ma'anar nahw ayaren larabci sunada gawan gaske sune kamar haka :
١) nufata
٢) misali
٣) yanki, gefe (side)
٤) abunda yake kusa
٥) nau'i, kala
٦) bayani
٧) Ma'ana D.S.D.S
Ma'anar nahw a ilmance shene ilimi wanda ke cike da ka'idoji , wanda ake Sanin hukunce hukuncen karshen kalmomin harshen larabci tundaga tsarin gininsu har'izuwa cancanzawarta.
2) ilimin nahw yana tattaunawa ne kan yadda kalma take hawhawa dakuma yadda take daya dayanta , dakuma chimakken bayani kan hauhawanta.
3) yana daga cikin aikin nahw shine ya kiyaye harshe daga tubatubai wanda harshe ke gudanarwa ayayi magana dakaratu musamman karatun AlQur'ani mai girma da haddissan mazon Allah(sw) kuma tahakane zaka fahimcesu.
4) yanada alawa dasauran ilimi guda 12 wanda sune:
@ sarfu @ arud @ insha'i @ luga @ rubutu @ bayan @ ma'ani D.S.D.S
5) na daga cikin falalarshi shine haskakawa mutu gurin fahimtar yaren Al-Qur'ani da haddissan manzon Allah. Domin ya tabbata daga bakin ayyubassuktayani yanacewa " wata baiwar Allah ta zama zindiqiya saboda rashin sanin da yaren larabci (ka'idojin nahw)
6) ilimin nahw ana amfani dashi ne tun gabanin zuwan musulunci, do min larabawa sune sukafi kowa fasahar yare, don haka sai Allah yaturo musu littafi wanda ya gagaresu kuma dayarensu haka manzon da aka tura musu
7) amma idan mukazo kan wanda yafara kirkiranshi to akwai zantut tuka mabnbanta.
Ance" abul_aswaduddu'li da umarnin amirul mu'uminin aliyu bin aby dalib (R.A)"
Kuma ance" a'a da umurnin umar bin kaddab
Kuma ance" ta hanyar ziyad bin abihi gun koyarda 'yarshi
Kuma ance" a'a Shi ya kirkira da kanshi bada umurnin kowa ba. Yafara da babin (topic) ta'ajeeb.
8) bayan ya gama yasa mishi suna ilimin NAHW
9) ana samun hukunce hukuncenshine acikin alqur'ani da haddissan manzon (s.a.w) dakuma wakokin larabawa kowa sunkasance kafirai.
0) hukuncinshi a shari'a shine idan Wani yayi zai iya dauke ma Wani (faradu kifaya). Amma fa wajibine akan dalinin ilimi.
Wadannan sune ginshikai dayakamata kasani dangane da ilimin nahw a takaice.
الكلام وما يتألف منه
كلامنا لفظ مفيد كاستقم *ورسم وفعل ثم حرف الكلم
Dukkan kalma datake bada ma'ana cikakiya itace ake cewa magana (kalam), shiyasa ibn malik yake cewa abunda ake cewa magana agunmu shine lafazi me dauke da Ma'ana sai Yayi misali da (استقم) Ma'ana (Mike).
Gudadayan kalam shine kalma (tilo) itakuma takasu kashi uku ne3 kamar yadda yace
واسم suna ( زيد، بيت،مكة)
وفعل aikatau ( قم، جذ، يذهب، يشم)
وحرف harafi (في، من،الى)
Alamun suna اسم
1 tanwin(=) 2 shigan lamun da alif(ال) 3 shigan haruffan jarri ( في، إلى من ك،ل،و،ث،رب) 4 karbar kasra(-) Alamun aikatau فعل 1 karbar (ت الساكنة) 2 karbar (سوف) 3 karbar (قد) Alamun harafi حرف
Shi rashin alamarshi itace alamarshi.
Kamar yadda sukace " harafi shine abunda baida alama ka'amsa wannan zancen zakazama masani"