Nau’ukan Kifi
Kifi wata halitta ce ta ruwa wadda galibi tana da ƙaya a waje da kuma cikin jikinta, wadda kuma take da ƙarni.[21] Ana kama kifi ne domin a ci kasancewarsa abinci mai gina jiki sosai. Akwai Karin magana waɗanda gaba ɗaya an gina tubalinsu ne kan nau’ukan kifaye da suke rayuwa a cikin gulabe da tafukka na wannan ƙasa. Misalinsu ya haɗa da:
v Tuhi ya gane gidan boɗami.
v Shagwaɓa, tarwaɗa da kukan ƙishirwa.
v Ƙurungu mugun kifi ko kura ba ta sa shi a baki.
v Ɗan harya alhajin ‘yan suka.
Waɗannan misalai na Basarken Karin Magana suna nuni zuwa ga wasu irin nau’ukan kifaye da suke rayuwa a cikin ruwan koguna da gulabe da tafukka na wannan guduma ta Sakkwato. Baya ga ambaton sunayen kifayen kamar tuhi da boɗami (gawo) da tarwaɗa da ƙurungu da harya, wannan rukuni na Karin Magana yana kuma nuna mana ɗabi’a da halayya ta wasu daga cikin kifayen. Misali, ƙurungu mugun kifi ne, ƙayar da yake da ita mai ƙwari ce sosai, harya kifi ne da ba baya yake ba wajen suka da ƙayarsa mai mugun dafi sosai. Tuhi da boɗami kuwa mazauninsu ɗaya a cikin ruwa sannan duk kowane daga cikinsu yana da dauriya ta zama a cikin muhalli na ruwa mai ɗamba.