Nuruddeen Gwadabe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Gabatarwa[gyara sashe | Gyara masomin]

Nuruddeen Gwadabe(1982-2005) tsohon shugaban daliban jami'ar Bayero ta Kano ne. Ya yi rawar gani a zamaninsa inda cikin ruwan sanyi ba tare da zanga-zanga ba ya kirawo mukaddashin shugaban jami'ar na wancan lokaci, Farfesa Maiwada zuwa makewayin dalibai domin ganewa idanunsa halin da su ke ciki. Hakan ta sa hukumar makarantar mai da kai wurin kyautata jin dadin dalibai. Haka kuma shi ne ya samowa kungiyar daliban jami'ar Bayero kyautar mota mai daukar fasinja talatin sabuwa dal har da AC daga gwamnatin Zamfara ana saura wata guda ya bar mulki amma ya dankata ga dalbai ba tare da ya karkatar da ita ba ko ya sauyata ya kawo tsohuwa kamar yadda aka saba.

Asali[gyara sashe | Gyara masomin]

An haifi Nuruddeen Gwadabe ne a unguwar Madungurum da ke birnin Kano, wadda akafi sani da yar mai shinkafi. Sunan Mahaifinsa Alhaji Rabiu Gwadabe, mahaifiyarsa Hajiya Rukaiyya Ibrahim Dasuki. Nurudden tagwai ne. Sunan dan uwan tagwaitakarsa Shamsuddeen Gwadabe, wanda a yanzu haka likita ne a asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano. Nuruddeen ya yi makarantar Islamiyya ta Gwadabe Maitasa da ke Yar Maishinkafi Kano kuma ya sauke karatun alkur'ani mai girma wurin Malam Sa'idu a Yola, jihar Adamawa. Daga nan ya cigaba da neman ilimin addini a duk inda ya samu kansa.

Karatun Boko[gyara sashe | Gyara masomin]

Nuruddeen Gwadabe ya fara Makarantar boko a Marsam Nursery school, Kano. Ya yi makarantun firamare na Kano Capital School,Kaduna Polytechnic Staff School, da Bayero University staff School. Ya fara karatun sakandare a Capital School, Yola ya kuma kammala a Command Day Secondary School, Rukuba, Jos. Daga nan ya shiga Jami'ar Bayero Kano inda ya fara da karatun share fage daga bisani kuma ya karanci ilimin fasahar kere-kere (Mechanical Engineering)a matakin digiri na farko.

Gwagwarmaya[gyara sashe | Gyara masomin]

Nuruddeen Gwadabe ya shiga gwagwarmayar kyautata rayuwar dalibai a jami'a inda ya rike mukamai da dama. Ya fara da mukamin Jami'in hulda da jama'a na kungiyar dalibai Musulmi ma su koyon aikin Injiniya, sai kuma Jam'in hulda da jama'a na kungiyar dalibai yan asalin jihar Kano, sai Sakataren Kudi na kungiyar dalibai Musulmi ta jami'ar Bayero kuma jami'in shirye-shirye na kungiyar dalibai Musulmi ta jihar Kano baki daya. Daga nan kuma aka zabeshi shugaban kungiyar daliban Jami'ar Bayero tare da nadashi mukamin shugaban kungiyar dalibai Musulmi ta jami'ar. Sai dai saboda nauye-nauyen da ke kansa bai iya samun damar karbar wannan nadin na Amir ba.

Rasuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

Nuruddeen ya gamu da rashin lafiya a zangon karshe na karatunsa na jami'a. A ranar da zai zana jarabawar karshe, ciwon ya tsananta aka mayar da shi gida. Bayan kwashe watanni hudu ana gwaje-gwaje a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano aka gano cewa cutar sankara ce ta kamashi. Daga nan aka turashi asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Shika, daura da Zaria. Daga karshe aka mayar da shi babban asibitin kasa da ke Abuja, inda ya rasu a can aka dawo da gawarsa Kano aka kuma binneshi a makabartar Dandolo da ke Goron Dutse. Allah ya jikansa da gafara.