Okechukwu Onuchukwu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Okechukwu Onuchukwu
Rayuwa
Sana'a
Sana'a Malami

Okechukwu Onuchukwu Farfesan Najeriya ne a fannin tattalin arziki kuma mukaddashin shugaban jami'ar ilimi Ignatius Ajuru ta jihar Ribas.[1][2]

Rayuwar farko da asali[gyara sashe | gyara masomin]

Okechukwu ya kammala karatunsa a jami'ar Fatakwal a shekarar 1990 inda ya karanta fannin tattalin arziki sannan kuma ya kammala karatunsa na biyu a fannin tattalin arziki a shekarar 1994.1994.[3]

Ya ci gaba da samun digiri na uku a fannin tattalin arziki a Jami'ar Fatakwal a shekara ta 1998.[4]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Okechukwu ya yi aiki a matsayin Dean, Faculty of Social Science, University of Port Harcourt.[4]

Ya kuma taba zama Darakta, Makarantar Kasuwanci ta Jami’ar Fatakwal da Shugaban Sashen Tattalin Arziki na Jami’ar Fatakwal.[5]

Gwamna Nyesom Wike ne ya naɗa shi a shekarar 2021 a matsayin mukaddashin mataimakin shugaban jami’ar ilimi ta Ignatius Ajuru. Nadin nasa ya fara aiki ne bayan nasarar kammala wa'adin tsohon mataimakin shugaba Farfesa Ozo-Mekuri Ndimele.[6][7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "UNIPORT VC CONGRATULATES OKEY ONUCHUKU ON APPOINTMENT AS ACTING VC, IAUE". www.uniport.edu.ng. Retrieved 2023-10-05.
  2. Uchenna, Okoro (2021-11-18). "Just In: Wike Appoints Professor Okechukwu Onuchukwu Acting Vice Chancellor Of IAUE". The Whistler Newspaper (in Turanci). Retrieved 2023-10-05.
  3. "Prof. Okechukwu Onuchukwu – Emerald Energy Institute" (in Turanci). Retrieved 2023-10-06.
  4. 4.0 4.1 "Prof. Okechukwu Onuchukwu – Emerald Energy Institute" (in Turanci). Retrieved 2023-10-05.
  5. Ele, Gideon (2021-11-18). "Governor Wike appoints Professor Okey Onuchukwu Acting VC Ignatius Ajuru University Port Harcourt –" (in Turanci). Retrieved 2023-10-05.
  6. Nigeria, Guardian (2021-11-19). "Wike appoints VC for Ignatius Ajuru varsity". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Retrieved 2023-10-05.
  7. "New Chancellor promises to add value to LAUTECH | Ladoke Akintola University of Technology, Ogbomoso, Oyo-State, Nigeria". www.lautech.edu.ng. Retrieved 2023-10-05.