Olivier Irabaruta
Olivier Irabaruta | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Muramvya (en) , 25 ga Augusta, 1990 (34 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Burundi | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | Dan wasan tsalle-tsalle, mawaƙi da long-distance runner (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 171 cm |
Olivier Irabaruta (an haife shi a ranar 25 ga watan Agusta shekarar 1990) ɗan wasan tsere ne mai nisan zango ɗan ƙasar Burundi. [1] A gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2012, ya fafata a tseren mita 5000 na maza, inda ya kare a mataki na 29 gaba daya a zagaye na 1, ya kasa samun tikitin zuwa wasan karshe.
A gasar Olympics ta lokacin zafi na shekarar 2016, y a yi gasar tseren mita 5000 da na mita 10,000. Ya kare a matsayi na 27 gaba daya a zagaye na daya na gasar tseren mita 5000 kuma bai cancanci zuwa wasan karshe ba.[2] Ya zo na 27 a gasar tseren mita 10,000.[3] Irabaruta ya kasance mai rike da tuta ga Burundi a lokacin parade of nations.[4]
Ya wakilci kasarsa a Gasar Cin Kofin Kasashen Duniya ta IAAF a shekarar 2009 a matsayin matashin ɗan tsere da kuma 2015, 2017, da 2019 a matsayin babban ɗan wasa.
A shekarar 2019, ya yi takara a tseren gudun fanfalaki na maza a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya na shekarar 2019 da aka gudanar a Doha, Qatar.[5] Bai gama tserensa ba.[5] [6]
Ya wakilci Burundi a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2020 a tseren gudun fanfalaki na maza.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |
- ↑ Olivier Irabaruta at World Athletics
- ↑ "Rio 2016" . Rio 2016 . Archived from the original on 2016-08-21. Retrieved 2016-08-25.
- ↑ "Rio 2016". Rio 2016 . Archived from the original on 2016-08-26. Retrieved 2016-08-25.
- ↑ "The Flagbearers for the Rio 2016 Opening Ceremony" . 2016-08-16. Retrieved 2016-08-25.
- ↑ 5.0 5.1 "Marathon Men − Final − Results" (PDF). IAAF . 5 October 2019. Archived from the original (PDF) on 27 June 2020. Retrieved 6 October 2019.
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedmen_marathon_results_world_championships_2019