Jump to content

Omar bn said

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

[1]KA SAN WAYE OMAR IBN SA'ID?[gyara sashe | gyara masomin]

Yana daga cikin Mus*ulman farko a kasar Amurka wadanda aka kamosu a matsayin ba*yi daga Afirka, wadanda suka yi sanadin samun Mus*ulmai a Amurka. Akwai darasi cikin tarihinsa. Wadannan hotunan da ma'anoninsu a cikin rubutun.

Omar ibn Sa'id malamin addinin Mus*ulunci ne wanda a shekarar 1807 aka kamashi a matsayin ba*wa daga kasar Senegal, ya rubuta tarihin rayuwarsa da larabci wanda ya bawa tur*awa mamaki domin ba su yi tsammanin akwai masu ilimi a Afirka ba a wancan lokacin. Wannan tarihin nasa ya bada damar sanin Mus*ulman farko na kasar Amurka. A lokacin da ya rubuta tarihin nasa yana da shekara 61.

An haifi Omar a Futa Toro ta Senegal, kuma ya karar da shekaru 25 din rayuwarsa wajen neman ilimi daga malaman addinin Mus*ulunci, ya karanci ilimin lissafi (Mathematics), ilimin sararin samaniya (Astronomy) da kuma kasuwanci (Business).

Daga cikin littafin tarihinsa ya rubuta cewar: "Azz*aluman mutane sun kamani, suka saidani ga Kir*istoci. Mun yi tafiyar wata daya da rabi a ruwa, sannan muka isa wani gari da ake kira Charleston (Amurka). Na fada hannun wani mutum azz*alumi wanda ba ya tsoron Allah, ba ya karanta littafin Allah (ba*ibul) ba ya kuma bautawa Allah".

Mus*ulman farko a Amurka sun fito ne daga bakaken fatan da aka kamo daga Afirka, Omar yana daga cikinsu.

Masana sun tabbatar da cewar, jirgin da ya dauko Omar ya iso garin South Carolina ne a shekarar 1807, a shekara ta gaba, kasar Amurka ta har*amta kasuwancin dauko ba*yi.

Omar ya gudu daga hannun azz*alumin mutumin da ya saye shi zuwa wani gari da ake kira Fayetteville da ke jihar North Carolina inda ya samu wani Co*ci ya fara bauta. Jami'ai sun kamashi zuwa gidan ya*ri, a lokacin ne Omar ya fara shahara bayan da aka sameshi yana rubutu a ginin gidan yarin da lar*abci, a tsammaninsu bakaken fata jah*ilai ne ba su iya rubutu da karatu ba.

Bayan fahimtar Omar na da ilimin larabci, sai wani sanannen mutum a wannan garin da ake kira Janar James Owen ya sayeshi a shekarar 1821, daga bisani Owen ya bashi ba*ibul na larabci, sannan ya bashi umarnin ya je Co*cin Presbyterian a masa wankan tsarki.

Mutanen yankin suka yita yabon Omar na komawarsa Kir*ista a tinaninsu, da kuma yadda ya rungumi addinin, sai dai a cikin Ba*ibul dinsa, Omar ya rubuta da larabci cewar: "Godiya ta tabbata ga Allah, duk wani alkhairi daga gare shi ne".

Omar ya yaudaresu ta yadda suna masa kallon wanda ya karbi add*ininsu, alhali ko a cikin ba*ibul dinsa sai da ya rubuta suratul fatiha, su kuwa suna yiwa surar kallon wata addu'a ce ta addinin Kiri*stanci ya rubuta da larabci. A wata takardar kuma ya rubuta wani sashi na Psalm da ke cikin bai*bul, a gefe guda kuwa ya rubuta addu'ar addinin Is*lama. Wannan ilimi nashi ya taimakeshi wajen boye addi*ninsa daga tur*awa.

A shekarar 1836 Omar tare da iyalan mai gidansa Owen suka koma Wilmington biyo bayan yakin basasa, ya rasu yanada shekaru 96, amma ba a san asalin dalilin mutuwarsa ba.[2][gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://docsouth.unc.edu/nc/omarsaid/summary.html
  2. https://www.baytalfann.com/post/the-autobiography-of-omar-ibn-said-a-muslim-slave