Jump to content

Owoidighe Ekpoatai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Owoidighe Ekpoatai
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

6 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019
Owoidighe Ekpoatai - Patrick Ifon
District: Eket/Onna/Esit Eket/Ibeno
Rayuwa
Haihuwa Jahar Akwa Ibom, 1966 (58/59 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Uyo Digiri, accounting (en) Fassara
Jami'ar jihar Imo MBA (mul) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Owoidighe Ekpoatai listen ⓘ (an haife ta a shekara ta 1966) 'yar siyasar Najeriya ce, 'yar majalisa kuma tsohuwar 'yar majalisar wakilai ta tarayya.[1] Ta wakilci mazaɓar tarayya Eket/Onna/Esit Eket/Ibeno na jihar Akwa-Ibom.[2] [3] An zaɓe ta a matsayin 'yar majalisar wakilai ta ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). A halin yanzu ita ce mai girma mai ba da shawara ta musamman ga gwamnan jihar Akwa ibom kan bunƙasa aikin gona [4] [5]

Owoidighe ta yi karatun sakandare a Makarantar Sakandare ta ‘Yan mata (GSS) AFANA kafin ta wuce Jami’ar Uyo, Uyo inda ta kammala digirin farko a fannin Accounting. A shekarar 2003, ta kammala digiri na biyu a fannin kasuwanci (MBA) a Jami’ar Jihar Imo, Owerri. [6]

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ta fara harkar siyasa ne a shekarar 2012 a matsayin ma’ajin jam’iyyar People’s Democratic Party a jihar Akwa-Ibom. [7] A watan Maris na 2015, an zaɓe ta a Majalisar Wakilai ta Tarayya don wakiltar Eket, Onna, Esit Eket da Ibeno Federal Constituency. [8]

An ba Owoidighe lambar yabo ta Justice of Peace a shekarar 2006 da kuma lambar yabo ta Ambassador of Peace a shekarar 2009. [7]

  • Jerin sunayen 'yan majalisar wakilan Najeriya, 2015-2019
  1. "I've not collected money for projects, says lawmaker". The Nation Newspaper (in Turanci). 27 December 2017. Retrieved 21 November 2020.
  2. "I have not collected money for constituency projects – Eket federal lawmaker". Vanguard News (in Turanci). 26 December 2017. Retrieved 21 November 2020.
  3. "Owoidighe Ekpoatai". The MasterList (in Turanci). Retrieved 21 November 2020.
  4. "2015 House of Representative Election Results in Nigeria". whowin.com.ng. Retrieved 21 November 2020.[permanent dead link]
  5. Nigeria, Media (28 April 2018). "List Of Members Of The House Of Representatives Of Nigeria, 2015 – 2019". Media Nigeria (in Turanci). Retrieved 21 November 2020.
  6. "Biography of Owoidighe Ime Ekpoatai". biography.hi7.co. Retrieved 21 November 2020.
  7. 7.0 7.1 "Hon. Owoidighe Ekpoatai biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 21 November 2020.
  8. "Election Centre". nigeriaelections.stearsng.com. Retrieved 21 November 2020.