Jump to content

Pablo mari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.


Pablo Marí Villar (An haifeshi a

ranar 31 ga watan Ogusta shekarar alif 1993), kwararren dan wasan baya ne dan kasar Sifaniya wanda yanzu haka yana taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Monza.

Dan wasan ya kammala karatun shi a makarantar kungiyar akademi ta Mallorca ta matasa. Dan wasanyayikungiyoyi da yawa a rayuwarsa a kasashe da dama. Kamar kasar Sifaniya, Nertheland, Ingila da kuma ƙasar Italiyabinda ya ci gasar Copa Libertadores da kuma gasar kofin SerieA.

A shekarar alif 2019 da kungiyar kwallon kafata Flamengo, ansa ɗan wasan a cikin jerin zakakuran yan wasan da sukafi kowa a shekarar.

Rayuwar Gida[gyara sashe | gyara masomin]

Mari da kuma matarshi mai suna Veronica Chacon suna da da mai suna Pablo Mari jr wanda aka haifa a shekarar alif 2018.

A ranar 27 ga watan Oktoba shekara ta alif 2022, Mari ya fadi inda yaji rauni a wurin siyayyana Carrefour a Assago, Metropolitan City a kasar Milan.

An kaishi asibiti a galabaice cikin wani irin mawuyacin hali a yanda mutane ke gani. Sai dai CEO na kungiyar ya fito yace dan wasan ankaishi ba cikin mawuyacin hali yake ba kuma zaiji sauki bada Jimawa Ba. Lokacin da aka kai harin, mutum 1 ya mutu, mutum hudu kuma sunji rauni. A lokacin wani mutumi ne mai matsalar kwakwalwa.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

https://en.wikipedia.org/wiki/Pablo_Mar%C3%AD