Jump to content

Rafiu Jafojo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rafiu Jafojo
Rayuwa
Haihuwa 1935
Mutuwa 2016
Sana'a

Rafiu Jafojo (6 Disamba 1935 - 23 Afrilu 2016) ɗan siyasan Najeriya ne. Ya kasance mataimakin gwamnan jihar Legas daga shekara ta 1979 zuwa 1983.[1]

Rayuwar farko da aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya yi aiki a matsayin mai duba gini a Hukumar Tsare-tsare ta garin Ikeja. Ya tafi Ingila A 1961 inda ya samu satifiket na shedar ƙasa a fannin Gine-gine daga Kwalejin Fasaha ta Hackney a 1966 da Higher National Certificate daga Brixon School of Engineering.[2] A cikin 1969, ya sami Advanced Certificate a Gine-gine daga Northern Polytechnic, Holloway (yanzu Jami'ar Arewacin London ) a 1970.[3]

A ranar 1 ga watan Oktoban 1979, Jafojo, tare da Lateef Jakande aka rantsar da shi a matsayin mataimakin gwamnan Legas na farko ta hanyar dimokuradiyya.[4]

An ƙaddamar da filin shakatawa na Rafiu Jafojo a Shasha Alimosho, Legas a watan Disamba 2017 don tunawa da Rafiu Jafojo.[5]

  1. admin (2016-05-14). "Rafiu Jafojo: Exit of an Awoist". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2022-05-28.
  2. "Jafojo... 80 Hearty Cheers To Former Lagos Deputy Gov". The Guardian Nigeria News – Nigeria and World News (in Turanci). 2015-12-06. Retrieved 2022-05-28.
  3. "Remembering Jafojo – The Nation Newspaper" (in Turanci). 2017-04-21. Retrieved 2022-05-28.
  4. "Ex-Lagos deputy governor, Jafojo dies at 80 – P.M. News" (in Turanci). Retrieved 2022-05-28.
  5. "Lagos Commissions Rafiu Jafojo Park".[permanent dead link]