Ranan Salla

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Ranar sallah rana ce ta farin ciki ga musulmai wacce take guda na sau biyu a kowace shekara.[1]

Sallah ta kasu kashi biyu, akwai Babbar sallah da karamar sallah.

Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]

Ita karamar sallah ana yinta ne bayan angama azumin watan ramadana, idan anga wata a daren 29 ko 30, toh washe gari za'ayi sallan azumi. Ita kuma babbar sallah ana yinta ne bayan azumi da wata biyu da kwana goma. Wato goma ga watan zul-hajji, washe garin arafa. Ana yanka rago, tinkiya, akuya, taure, saniya, ko rakumi.

Ranar karama sallah wato sallar azumi. Da safe bayan ankarya kowa zaiyi wanka ya sanya sababbin kaya, aje masallaci domin guda nar da sallar idi. Su kuma iyaye mata za suyi girki na musamman da za'aci a gida da kuma rabawa 'yan uwa da abokan arziki. Ranar sallah kowa yana samun abunda zaici. Ranace ta musamman ga Al’umar musulmai gabaki daya.

Babban Sallah[gyara sashe | Gyara masomin]

Ranar babbar sallah/sallar layya. Ranar sallah da safe kowa zaisa kayan sa mai kyau,amma anfin son fararen kaya ga Wanda Allah ya hore ma wa,amma kuma zaka iya sa kalan da kake so ba laifi bane,Amman idan mutum yana da halin layya ana so ya kame bakin sa harsai an sakko daga masallaci bayan babban limamin ya yanka ragon sa. Idan ansauko wato andawo daga masallaci, sai duk wadda yakeda abun yanka ya yanka dabbar sa. A kasar hausa, ranar za'a rataye ragon sai washe gari ayi aiki, shikuma kayan ciki zasu sarrafashi a soya kowa ya taba. Washe gari za'a sauko da dabbar da aka rataye a yayyanka a bawa yara su rarrabawa makota da 'yan uwa. Sauran naman za'a dafashi a soya a rarrabawa mutanen gida kowa ya dauki rabon sa. Shi kuma kai da kafafun dabbar za'a babbake a ajiye sai bayan yan kwana ki ayi gandarsa aci. Wasu kan ajiyeshi sai lokacin takutaha wanda shima wani al-adane na hausawa.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. "Eid al-Fitr: Abubuwan da ake so Musulmi ya yi kafin Sallar Idi". bbc hausa. 12 May 2021. Retrieved 25 August 2021.