Rashid Abdullah Al Nuaimi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rashid Abdullah Al Nuaimi
foreign minister (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa 1937 (86/87 shekaru)
ƙasa Taraiyar larabawa
Karatu
Makaranta Cairo University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya da ɗan siyasa

Rashid Abdullah Al Nuaimi (راشد عبدالله النعيمي ) tsohon ministan harkokin wajen kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ne.

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Nuaimi memba ne na dangin Ajman mai mulki, Al Nuaimi.[1] Yana da digiri na farko a injiniyan man fetur, wanda ya samu daga jami’ar Alkahira a shekarar 1967.[2]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Nuaimi ya fara aikinsa ne’a sashi mai zaman kanta a masarautar Abu Dhabi.[2]Sannan ya shiga ma'aikatar harkokin waje ta Emirati kuma har zuwa shekarar 1975, ya yi aiki a can a fannoni daban -daban.[2]  A shekarar 1975, an nada shi a matsayin daraktan sashen harkokin siyasa a ma'aikatar harkokin waje.[2]  A cikin shekara ta 1976, ya zama sakataren harkokin waje. Ya rike mukamin karamin ministan harkokin waje daga shekarar 1977 zuwa shekara ta 1990.  Hamdan bin Zayed ya gaje shi a mukamin.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Rashid bin Abdullah Al Nuaimi". APS Review Gas Market Trends. 8 June 1998. Retrieved 15 April 2013.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 "Profile". ECSSR. Archived from the original on 11 September 2016. Retrieved 15 April 2013.