Rattlesnake (fim na 1995)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Rattlesnake fim ne na shekarar 1995 na Najeriya wanda Amaka Igwe ya rubuta kuma ya ba da Umarni, sai Austin Awulonu ya shirya shirin. Wannan shine karon farko da Amaka Igwe ya fara yin fim mai tsayi kuma an yi shi kashi 3. [1] Taurarin shirin sun haɗa da Francis Duru, Okechukwu Igwe, Nkem Owoh, Anne Njemanze da kuma Ernest Obi. [2]

Takaitaccen bayani[gyara sashe | gyara masomin]

Rattlesnake ya ba da labarin Ahanna Okolo wanda ya rasa mahaifinsa a cikin yanayi na tuhuma tun yana yaro kuma ya shiga cikin rayuwar aikata laifuka. Bayan rasuwar mahaifinsa, kawun Ahanna ya zama ubansa yayin da yake auren mahaifiyarsa. Kawun Ahanna ya aika Ahanna da ƴan uwansa ƙauye a lokacin da ya karbe dukiyar baban Ahanna a Legas. Ahanna ya tsunduma cikin aikata laifuka tare da yiwa samar wa ƴan uwansa kudaden da ya samu na mu’amalar da ya yi na aikata laifuka. Ya ci gaba da rayuwa biyu a matsayinsa na ɗan kasuwa mai mutunci kuma ɗan fashi da makami a bayan fage. Duk da haka ya zama mutum mai mutunci a cikin al'umma lokacin da aka fallasa baƙar mu'amalarsa. [1]

Yan wasan kwaikwayo[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 Empty citation (help) Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  2. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :1