Rigasa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Rigasa[gyara sashe | gyara masomin]

Tashar jirgin kasa Kaduna zuwa Abuja da ke cikin garin Rigasa

Nasan mai karatu musamman wadanda ba a garin Rigasar suke ba ko kuma jahar Kaduna zasu bukaci sanin wani abu game da ita Rigasar.

Rigasa  ƙauyen birni ne da ke karamar hukumar igabi a yankin Kaduna ta tsakiya a cikin jahar Kaduna, Kaduna, Nigeria. Na kira yankin ne da KAUYEN BIRNI saboda wasu ƴan dalilai wanda zan bayyana su a nan gaba.

Garin RIGASA yana daya daga cikin yanki mafi girma da yawan jama'a a Najeriya, tare da kiyasin kimanin mutane miliyan uku ne suke rayuwa a cikin sa. yana dauke da yankuna kamar su, Danmani, Nariya, Makera, Mashi, Hayin Malam Bello, Sabon-garin Rigasa, Kwate, Mai-giginya, da sauransu.

Yana da fadin kusan kilomita 14 zuwa 8. Rigasa yana daya daga cikin unguwanni 255 na jihar Kaduna

Garin Rigasa yana da manyan makarantun firamare da sakandare kama daga na gwamnati da masu zaman kansu masu tarin yawa, yana da makarantun islamiyyu suma masu yawan gaske duk a cikin garin Rigasar

Haka kuma yanzu haka akwai tashar jirgin karsa  daga Kaduna zuwa Abuja wanda wannan tashar tana cikin garin Rigasar ne.

An yi imanin cewa Rigasa na karbar bakuncin manyan baki irin su Shugabanin siyasa, sarakuna, Air Vice Marshal Maisaka (marigayi), Shugaban Karamar Hukumar Igabi, ba tare da ambaton wasu Farfesa da Likitoci da dama da ke zaune a cikin garin ba.

A yanzu haka  Rigasa tana da mahaddata Alkur'ani masu yawan gaske, manyan likitoci, manyan ƴan siyasa, malamai, yan jarida da dukkan wani nau'i na masu ilimin kimiyya da fasaha.

Kafin rikicin addini na 2000 a jihar Kaduna, akwai kabilu da yaruka masu yawa a cikin Rigasar wanda a halin yanzu anyi ittifakin hausawa ne mafiya yawa a cikin garin kuma al'adar Hausa itace al'adar wannan yanki. kashi 90% na al'ummar wannan yanki musulmai ne.

Unguwannin Rigasa.[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Danmami
  2. Abuja road
  3. mashi Gwari
  4. Dattawa
  5. Ƴankifi
  6. High land (ailan)
  7. Ado gwaram
  8. Ƴan rumfar
  9. Lokoja
  10. Makera
  11. Zariya road.
  12. hayin Malam bello
  13. unguwar turaki
  14. Makarfi road
  15. Nariya
  16. Mai giginya
  17. Garin igabi
  18. Kwate
  19. jumare road
  20. unguwar adarawa
  21. Rimi
  22. Daura road
  23. Naira road
  24. Layin zawarawa
  25. Layin bola
  26. Layin cinema
  27. Taro-taro
  28. Unguwar matasa
  29. unguwar ƴan allo
  30. Da sauran su.

Kasuwannin Rigasa[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Kasuwar ƴan Gwari
  2. Kasuwar kashen kwalta Rigasa
  3. Kasuwar layin lokoja
  4. Musaiyaf plaza

Shahararrun mutane na Rigasa[gyara sashe | gyara masomin]

  1. jabir khamis Rigasa (shugaban karamar hukumar igabi)
  2. Bashir Musa dan baturia (sakataren jam'iyar PRP Kaduna)
  3. Barr. Sani Shehu sunusi (lauya mai zaman kansa)
  4. Alh. Aliyu dogara ga Allah (dan kasuwa /dan siyasa)
  5. Marigayi mal Aliyu adam kuchi (malamin addini)
  6. Dr. Yusuf arrigasiyyu (shugaban hukumar alhazzai Kad.)
  7. Hajiya Rakiya danladi jumeta (yar siyasa)
  8. Mal. Adam Muhammad maitagode. (Malamin addini)
  9. Mal Kabir ilyas .
  10. Abdulrasheed Rabi'u Rigasa (marubuci/ mai biciken tarihi/ mai koyan aikin jarida)
  11. mal.Muhammad Alkhamis(mai-fada aji/malanim addini/shugaban makarantar ahlus-suffah)

Kungiyoyin Rigasa[gyara sashe | gyara masomin]

[gyara sashe | gyara masomin]

  1. star City youth foundation
  2. dan baturia foundation
  3. RAAF

Makarantun Rigasa[gyara sashe | gyara masomin]

  1. LEA. Lokoja road Rigasa
  2. LEA mashi Gwari Rigasa
  3. GSS. Tankin Ruwa Rigasa
  4. Maitagode memorial college
  5. Sardauna memorial academy
  6. Madrasatu Adamu Abdullahi
  7. [./Usman_memorial_academy_Rigasa_0802_409_2753_https://maps.app.goo.gl/7u5hXRp4gYhynvUk8 Usman memorial academy Rigasa]
  8. Ahlus-suffah college of education (NCE)

Muhimman wurare na Rigasa[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Tashar jirgin kasa Kaduna zuwa Abuja
  2. Police station Rigasa
  3. Babban Asibitin Rigasa (Rigasa General hospital)
  4. Gidan Hakimin Rigasa
  5. Gidan sarkin makera Rigasa
  6. gidan sarkin arewa Rigasa
  7. Gidan sarkin mashi-gwari

Changing Yanayi a Rigasa (climate change)[gyara sashe | gyara masomin]

Gundumar Rigasa wacce take gargashin Garamar hukumar igabi a cikin Garin kaduna ta fuskan tar mastaloli na changing yanayi musamman ma idan lokacin Ruwane ku kuma lokacin zafi.

Lokacin Ruwa yana lalata hanyuyi da kuma gidajen da mutane suke kwana a cikinsa.

Unguwannai daban daban a cikin gundumar sun lalace tasana diyya tashin hanyoyin ruwa dakuma Wada tattun gada wacce muyane suke hawa dumin stallaka hanya. Misali a unguwar Enkilishi, makera, lokoja, Daura road, gadar bilatu da unguwan hayin Amina dama sauran su suna fuskan tar mastanacin zaizayan gasa.

zaizayan gasa na hayin Amina.
zaizayan gasa a hayin amina


[gyara sashe | gyara masomin]