Rowa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rowa


Wuri
Map
 53°29′15″N 13°16′08″E / 53.4875°N 13.268889°E / 53.4875; 13.268889
Ƴantacciyar ƙasaJamus
Federated state of Germany (en) FassaraMecklenburg-Western Pomerania (en) Fassara
Rural district of Mecklenburg-Vorpommern (en) FassaraMecklenburgische Seenplatte District (en) Fassara
Non-urban municipality in Germany (en) FassaraHolldorf (en) Fassara
Labarin ƙasa
Yawan fili 5.52 km²
Altitude (en) Fassara 89 m
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 17094
Kasancewa a yanki na lokaci
Tsarin lamba ta kiran tarho 039603

ROWA

GABATARWA Da sunan Allah Mai rahama, Mai jinkai, Mai kowa, Mai komai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban ma’aika, Annabi Muhammadu (S.A.W).

Wannan muqala, na da kudurin yin tsokaci a kan dabi’ar rowa da matsayinta a rayuwar Bahaushe jiya da kuma yau. Haka kuma tare da fito da irin sauye-sauye da rayuwar Bahaushe ta samu dangane da dabi’ar rowa. Bayan haka, za mu dubi dalilan da suka kawo wadannan sauye-sauye.

Baza mu yi kasa a gwiwa ba wajen nuna illolin rowa da kuma sakamakon da takan haifar a al’umma. A wannan nazari, zan dubi rowa ta kusurwowi uku kamar haka: - A mahangar Al’adar Bahaushe, da Mahangar Zamani, sannan ta Mahangar Addinin Musulunci. Bisa wannan dalili ne yasa na yi wa wannan maqalar take da “Rowa (Hali, ko Wayau, ko Ciwo?)”.

Na kawo taken a matsayin tambaya ne don ya ba mu damar lalubo amsa. Tare da fatan mai karatu ko saurare zai gano ko zakulo amsar a karshen muqalar, don samun mafita ko a fid da jaki a duma.

FASHIN BAkI.

ROWA:- Na nufin wata dabi’a ce wadda mutum kan yin a hana ko kin baiwa kowa wani abin hannunsa. A kan kira namiji da marowaci, mace kuma marowaciya, idan jam’i ne kuma a ce musu marowata.

HALI: Na nufin dabi’a wadda aka san mutum da ita wadda yake aikatawa yau da kullum.

WAYAU: Na nufin kaifin tunani wanda mai shi ya kan yi amfani da shi idan wani al’amari ya taso masa don samun mafita. A wani lokaci akan kira wayau da dabara.

CIWO: Na nufin wani bakon sauyi mara dadi mai tafe da zugi da ya kan samu jikin mutum ko dabba, ko tsuntsu ko tsirrai. Akwai ciwo na sarari watau na zahiri, sannan akwai ciwo na ɓoye ko na ma’ana wanda ba a iya gani da ido.


Madogara: [{Dakta Mu'azu Sa'adu Muhammad Kudan, Shugaban Sashen

Koyar da harsunan Najeriya a Jami'ar Sule Lamido Kafin Hausa Jihar Jigawa}]