Rubutun adabi
Rubutun adabi zuwan ilimin karatu da rubutu cikin al'umman Hausa ya sauya hanyoyin rayuwarsu na yau da kullum kafin muyi nisa, ya kamata mu san daga ina hausawa suka sami ilimin karatu da rubutu?
Shi dai hanyoyin rubutu iri biyu da hausawa ke amfani da su.Dukkan wanɗannan hanyoyi biyu kuwa baƙi ne. Hanya ta farko itace hanyar rubutu na ajami na biyu itace rubutun boko.
Rubutun Ajami
[gyara sashe | gyara masomin]Rubutun ajami ya samu asali daga harufan Larabci.zuwan addinin musulunci shi ya haddasa ake amfani da harufan Larabci don akoyi karatun Alkur'ani da sauran littattafai addinin Islama.Hausawa sun ari wanɗanan harufan su ka juyashi izuwa ga Yaren Hausa domin su gudanar da Rayuwar su a bangaren rayuwar su da kuma cinikayya, Rubutun ajami ya kai aƙalla shekaru fiye da ɗari da hamsin Hausawa suna amfani da irin wannan hanya ta rubutun ajami kafin zuwan rubutun boko.
Rubutun Boko
[gyara sashe | gyara masomin]Kamar yadda addinin musulunci ya zamo shigowar Larabci, hakama larabci yayi sanadin samuwar rubutun ajami, yadda Larabci ya samu asali aƙasar Nigeria, shima rubutun boko ya samu ya shigo cikin maƙwabtan Hausawa na kudancin kasar nan Nigeria ta fuskar addinin masihanci wato kiristanci, har ta kai da ana koyan shi amajami'u wato chochi, yankin kasan nan ne suka fara karatun boko ta yadda sukayi nisa ga mutan arewa a wajen karatun boko, har takai a yau arewacin Najeriya sun kai mutuqa awurin rubuce-rubuce afannin siyasa da al'adar.