Rukunan Bahi Rock-Art
Rukunan Bahi Rock-Art | ||||
---|---|---|---|---|
Wuri | ||||
|
Samfuri:Infobox historic site Shafukan fasaha na Bahi Rock-Art ko zane-zanen dutsen Bahi zane-zanen dutse ne da ke wurare uku a yankin Dodoma na ƙasar Tanzaniya. [1] [2] Ana kuma kyautata zaton cewa waɗannan fararen zanen kayayyakin mutanen Wamia ne, wadanda suka mamaye yankin kafin mutanen Wagogo (mazauna yanzu) Zane-zanen da ke nuna shanu, da sifofin mutane, kwarangwal, gou, tsuntsu, da kibiya, da dai sauran alamomi, ana zaton an aiwatar da su ne a lokuta masu muhimmanci kamar jana'izar. [1] [2] Mutanen Wagogo, duk da cewa ba su da cikakkiyar masaniyar ainihin mahimmancin zanen ga Wamia, sun ci gaba da amfani da wuraren a matsayin wurare masu tsarki don bukukuwan,damina . An kiyasta cewa zane-zanen Bahi ya kai shekaru akalla guda 340 bisa ga tarihin sarkin Bahi a shekarar 1929, wanda ya bayyana kiyasin lokacin da kakansa, Kimanchambogo,ya isa yankin. [1] Hanyar zanen fari gabaɗaya tana da alaƙa da yawan noma na Bantu. [3]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Kondoa Rock-Art Shafukan
- Rukunan Tarihi na Ƙasa a Tanzaniya
Nassoshi
[gyara sashe | gyara masomin]Samfuri:Navbox prehistoric cavesSamfuri:National Historic Sites of Tanzania