Jump to content

Rukuni:Tarihi akan zamani

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Tarihin Zamanin Jahiliyya Larabawa a wancan lokacin -na jahiliyya- ba su kasance ma'abuta littafi ko mabiya wani saukakken addini ba, balle har -littafin ko addinin- ya daga matsayinsu na tunani, zamantakewa da wayewa. Jahilci da duhun kai da karkacewa ne kawai suka mamaye tsibirin larabawa, kuma suke wasa da hankula da akida. Larabawa sun kasance suna bautar gumaka, aljanu, taurari da Mala'iku; kadan daga cikin su ne suka kasance a kan addinan Annabi Ibrahim, Musa da Isa (a.s).

A irin wannan halin al'ummun da suka fi labarawa wayewa da ci-gaba, wato Yahudawa, Nasarawa da Majusawa, suka kasance. Su ma sun kasance karkashin kamun rayuwar jahiliyya, bata da karkacewar akida da zaluncin siyasa. Suna karkashin masu dagawa. Akwai wasu manyan dauloli uku da ke kewaye da larabawa. Akwai daular Rum daga yamma, daular Farisa daga gabas, sai daular Habashawa daga kudu. Wadannan su ke da karfin siyasa da wayewa a wancan lokacin. Kasancewar larabawan da ke garin Makka da kewaye ba su san ma'anar hukuma ba, sun kasance suna raye karkashin mulkin kabilanci da shugabancin wasu manya masu karfi a kan talakawa da bayi. [1] A irin wannan duhun zamantakewa, mace ta kasance tana dandana rayuwar wahala da rashin mutunci. Ba ta da hakki, ba daraja; saboda ita, a al'adar wannan al'umma ta jahiliyya, mallakar namiji ce, ana gadon ta kamar yadda ake gadon dabbobi da abubuwan mallaka. 'Ya'ya sun kasance suna gadon matan ubanninsu kuma su aure su. Dayan su ya kasance idan aka haifar masa 'ya mace sai bakin ciki ya rufe shi, ya shiga tsoron kunyata da bacin suna, sai ya dauki matakin kashe ta ko bisne ta da rai ko ya karbeta cikin wulakanci da kiyayya. Yayin da muka fahimci wannan hakika, za mu iya fahimtar Musulunci da girman Annabinsa (s.a.w.a); wanda, bisa yardar Allah, ya iya ceto dan Adam da sanya shi a kan hanyar madaukakiyar wayewa da daidaituwar dabi'a da shiriya.

Tarihin Kasar Hausa

[gyara sashe | gyara masomin]

Masana tarihi sun ambaci cewa, akwai mutane tun lokaci mai tsawo da ya shude a wadannan garuruwa na Kasar Hausa, kuma babu wanda zai bugi kirji ya ambaci daga inda suke, koda yake dai wasu kuma sun ambaci cewa ana kyautata zaton asalin Hausawa barbarar yanyawa ne tsakanin mazauna kasar da baki da suka yiwo kaura daga kasashen Asiya zuwa kasashen Afirka.

Dalilin wannan kaurar kuwa, an ce wai juyin mulkin da ya faru ne a tsakanin Banu Abbas da Banu Umayyah a Bagadaza, shi ya sanya wasu suka yiwo kaura, daga nan ne suka bazu cikin Afirka ta Yamma, musamman ta fuskar kasuwanci. Sai dai kuma an ce, yayin da suke yin wadannan kaurace-kauracen ne, kamanninsu da harshensu da al’adunsu suka canja saboda auratayya da canjin yanayin rayuwa.

Har ila yau an kara da cewa, ana zaton mutanen sun fi dadewa a Daura da Kano, ba don komai ba kuwa sai don su ne aka gwada kuma aka ga akwai dadadden tarihinsu da yadda mutanen suka rayu a wadannan wurare. [2].

Akwai masu ra’ayin cewa, tun asali Hausawa a garuruwansu na kasar Hausa Allah ya yi su, ba wai sun yiwo hijira ba ne daga wani wuri suka zo nan din. Malaman suna da hujjoji masu yawa a kan hakan, daga ciki suna kafa hujja da maganar babban Malamin nan Sheikh Nasiru Kabara, kamar yadda yake cewa jirgin kwale-kwalen Annabi Nuhu (AS) yayin da ruwan Dufana ya dauke ya tsaya ne a wani gari mai suna ‘Yandoto, wanda yanzu garin yana cikin Jihar Zamfara ta nan kasar Hausa.

Asalin Kalmar Hausa da Ma'anarta

[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai maganganu da yawa dangane da asalin kalmar Hausa, inda suka bayyana a matsayin ra’ayinsu. Daga cikin maganganun akwai:

Nil Skinner (1968) cewa ya yi, “Asalin kalmar Hausa, an samo ta daga Songhai. A ganinsa, akwai dadaddiyar dangantaka tsakanin Hausawa da su mutanen Songhai, har ta kai Hausawa suna aron kalmomin Songhai domin a nasa binciken cewa, kalmar Hausa an samo ta ne daga ‘Assa’ sunan da suke kiran mutanen da suke Gabas da su, su kuma Hausawa suka aro suka lakaba wa kansu.

Malam Aminu Kano kuwa, ya bayyana cewa an samo kalmar Hausa daga kalmar Habasha, wai don a cewar sa asalin Hausawa mutanen Habasha ne, kuma a maimakon a rinka cewa Habasha din sai ake cewa Hausa. [3].

A nasa tsinkayen, Mr. C.R. Niben (1971) cewa ya yi, an samo asalin kalmar Hausa ne daga Buzaye, domin kuwa haka suke kiran mutanen dake zaune a arewacin Kogin Kwara, wato Hausa. [4].

Shi kuwa mai Martaba Sarkin Ningi; Alhaji Haruna Wakati, cewa ya yi an samo kalmar Hausa ce daga labarin zuwan Bayajida garin Daura, a lokacin, da ya isa da daddare ya sauka a gidan wata tsohuwa ‘Ayyana’ ko kuma ‘Wayre’, inda ya bukaci ruwan sha a wurinta, da cewar ba ta da ruwa ya tambaye ta ina zai samu, ita kuma ta sanar da shi babu inda zai samu sai ya je rijiya, kuma matsalar ba a diban ruwa sai sati-sati ake zuwa a debo ruwa; saboda wata macijiya mai suna sarki.

Siffofin Bahaushe da Halayensa

[gyara sashe | gyara masomin]

Bahaushen mutum baki ne amma ba baki kirin ba irin wadanda Turawa ke kiran su Negroid, domin su bakin su wankan tarwada ne. Bahaushe ba shi da dogon gashin kai irin na mutanen Songhai, amma kirar jikinsa da kamanninsa daidai yake da na al’ummar Aryaniyawa (Aryan), wadanda da suke zaune a tsakanin kasashen Turai da Asiya, kafin su yi hijira su watsu wurare daban-daban a duniya. Game da halayensa kuwa, halaye ne na nagarta wadanda ya shahara das u, kuma yana daya daga cikin shahararrun kabilun da ake girmamawa a Afirka. Wadannan halaye na Bahaushe su suka daga shi har ya yi fice aka san shi a duniya ta da, da ta yanzu fiye da sauran kabilun bakar fata a Afirka ta Yamma. [5].

== Shugabanci na nufin rikon ragamar al’umma da ba su umarni da yi musu jagoranci bisa tafarkin da suka amince da shi, da tsara musu dokoki da sasanta tsakaninsu, da makamantan wadannan. Shugaba shi ne kololuwa a tsakanin al’umma, wato shi ne yake saman kowa, umarninsa ake bi, shi ne mai zartar da hukunci a tsakanin al’umma. A Kasar Hausa kuwa, akan samu sarki a matsayin shugaba, sai kuma ‘yan fadarsa wadanda su ne masu taimaka masa wajen tafiyar da al’amuran jagorancinsa.

Shugabanci ta bangaren al’adun Hausawa kuwa, ya faro ne daga tsarin zaman iyali inda maigida yake kamar sarki a gidansa, wanda shi ne babba, daga nan sai matarsa da sauran yaran gida. Yayin da aka samu gidaje biyu ko fiye da haka akan zabi wani dattijo a matsayin shugaba, ko kuma wani jarumi wanda ya nuna ya fi kowa sadaukantaka da jaruntaka da dauriya. Wasu dalilai kamar halin kunci a cikin gida ko bukata irin ta tsaro ko rashin zaman lafiya, kan sa maigida ya fitar da wasu daga cikin ‘ya‘yansa zuwa wani wuri na daban, kamar gona ko garke. Ta haka ne iyali kan yadu su yawaita su hada wani kauye. Saboda haka ne sai a kara zabar wani shugaban da zai shugabanci wannan kauye. Wannan shi ya haifar da mukamin Mai Unguwa kuma shi zai rinka tsara musu dokoki.

Kauye yakan bunkasa ya zama gari sosai, a sakamakon haka sai a kara zabar wani mutum a matsayin Maigari (Fagaci) domin kula da wannan gari. Da aka samu ci gaba kuma, garuruwa suka kara yawaita sai aka samar da mukamin Hakimi, ana ba wa Hakimi garuruwan Maigari akalla guda biyar don ya kula da su. Da tafiya ta yi tafiya, sai aka samar da mukamin Sarki, inda ake hada wa Sarki masarautar Hakimai akalla biyar ko fiye domin ya shugabance su ya kuma shimfida musu dokoki domin zaman lafiya.

  1. http://www.alwilayahnews.net/index.php/tarihi/tarihin-ahlulbaiti-a-s/manzon-allah-muhammad-bn-abdullah-s-a-w-a/80-yanayin-larabawa-kafin-aiko-annabi-s
  2. (Adamu, M.T. 1997:21 – 22)
  3. (Adamu, M.T. 1997:19)
  4. (Adamu, M.T. 1997: 19)
  5. (Kantoma, 2011:16-17)
A halin yanzu babu shafuka a wannan category.