Jump to content

SALLAR KISFEWAR RANA

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

SALLAR KISFEWAR RANA

a. Ma’anar kisfewa, Hikimar shar’anta ta.

Kusufi: shi ne bacewar hasken rana ko wata. Kuma yace daga cikin ayoyin Allah Ta’ala inda ke jan hankalin mutum zuwa ga kimtsawa da kuma lura da cewa lalle Allah Ta’ala yana kallon kowa, da kuma neman mafaka a gare shi a lokacin rikicewar yanayi da kuma yin tunani akan girman hukuncin Allah ta’ala ga wadannan halittu.

 Kuma da cewa lalle shi ne kadai wanda ya cancanci a bautawa masa.

 Idan rana ta kisfe (wato haskenta ya bace) ko kuma wata ta kisfe (wato haskensa ya tafi), sallar kisfewa ta zama Sunnah ga jama’ah.

﴿وَمِن ءَايَتِهِ ٱلَّيلُ وَٱلنَّهَارُ وَٱلشَّمسُ وَٱلقَمَرُ لَا تَسجُدُواْ لِلشَّمسِ وَلَا لِلقَمَرِ وَٱسجُدُواْ لِلَّهِ ٱلَّذِي خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُم إِيَّاهُ تَعبُدُونَ٣٧﴾

 Ma’ana:“Daga cikin ayoyin Allah akwa dare da yini, rana da wata, kar ku yi sujjuda ga rana ko ga wata, ku yi sujjuda ga Allah wannna da ya halicesu, in kun kasance shi kuke bautawa”. (Fusilat: 37)

b. Lokacinta.

 Daga lokacin da aka samu kisfewar rana ko wata zuwa wucewar hakan, kuma ba’a ranka ta in lokacin ta ya wuce, kuma ba a ruwaito yin umarni da yinta ba bayan hasken ya bayya, saboda lokacin ya wuce.

c. Siffarta.

 Raka’a biyu ce za’a karanta fatiha a raka’ar farko a bayyane da kuma surah mai tsawo, sai ayi ruku’u mai tsawo, sai kuma a dago daga ruku’in sai ayi tasbihi hadi da gode wa Allah, sa’annan a karanta fatiha da kuma surah mai tsawo, sai a sake yin ruku’i, sa’annan kuma a dago, sai ayi sujjuda biyu masu tsawo, sa’annan kuma sai a sake sallatar raka’a ta biyu kammar yadda aka yi ta farko. Amma mafi kasa da ta farko a dukkanin ayyuka (wato raka’a ta biyu ba zata kai ta farko ba), sallar kisfewar rana tana da wata siffar kuma banda wannan wacce ake yi. Saidai amma wannan ita ce wacce ta tabbata kuma tafi ciki, idan kuma ya yi ruku’u uku ko hudu ko biyar babu laifi idan bukatar hakan https://islamhouse.com/read/ha/fikhu-a-sawwake-2778721#t27